Gwamnonin G5 na PDP za su mara wa Tinubu baya a 2027 – Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Benuwe, Samuel Ortom ya ce, gwamnonin G5 na Jam’iyyar PDP za su sake marawa takarar Shugaban Kasa Bola Tinubu baya a 2027 idan ya ce zai sake tsaya wa takara.

Mista Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata liyafar cin abinci ta murnar shiga sabuwar shekara da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya shirya a Jihar Ribas.

Gwamnonin G5 sun hada da Mista Ortom, Mista Wike, tsohon gwamnan Jihar Inugu, Ifeanyi Ugwuanyi, tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu, da gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde.

Mista Ortom ya ce, G5 ba su yi nadamar goyon bayan Tinubu a zaven 2023 kuma za su mara masa baya a karo na biyu idan ya fito takara.

”To ku saurare mu da kunnen ku bibbiyu, jagoran tafiyar G5 ya fadi cewa a 2027 dukkan mu Tinubu za mu yi. Saboda haka mu tun yanzu mu san inda muka dosa.

”Ba gara ma Tinubu ba da shi gogaggen dan siyasa ne kuma haziki a harkar gudanar da mulkin jama’a. Za mu bishi. Domin mun bi gwamnatin baya da ta jizgo Nijeriya daga can sama ta naka ta da kasa sannan ta kara gaba.