Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwarzon dan kwallon tawagar Jamus, Franz Beckenbauer ya rasu, yana da shekara 78 a duniya.
Ya dauki kofin duniya a matakin kyaftin din Jamus a 1974, da kuma a matsayin koci a 1990.
Tsohon mai tsaron baya ya buga wa Bayern Munich wasa 582, kuma ya lashe babban kofin gasar Jamus a matakin dan wasa da kuma a matsayin koci.
Dan kwallon wanda ake yi wa lakabin Der Kaiser, ya lashe European Championship a matakin dan wasa a 1972, kuma ya lashe Ballon d’Or karo biyu.
Beckenbauer, wanda ya fara taka leda a matakin dan wasan tsakiya ya fuskanci Sir Bobby Charlton a gasar kofin duniya a 1966, inda Ingila ta lashe kofin da ci 4-2 daga nan ya koma buga gurbin dan baya.
Ya kuma ci kwallo hudu a gasar kofin duniya a 1966, lokacin yana da shekara 20, shi ne kuma ya lashe kyautar matashin dan kwallo a gasar.
Ya buga wa tawagar West Germany wasa 103.
A matakinsa na dan wasa a Bayern Munich ya lashe kofin babbar gasar Jamus hudu da European Cup a 1974 da 1975 da kuma 1976.
Ya kuma dauki Bundesliga a kungiyar Hamburg.