Mun yi na’am da hukunce-hukuncen Kotun Ƙoli – APC

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyyar APC ta ce ta yi na’am da hukunce-hunkuncen da Kotun Koli ta yanke kan kararrakin da aka daukaka na kalubalantar sakamakon zaben gwamnoni na 2023 a jihohi guda takwas.

APC ta bayyana gamsuwarta ne cikin sanarwar da ta faitar ranar Juma’a mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na Kasa, Felix Morka.

Jam’iyyar ta ce ta yi matukar farin ciki kan yadda kotun ta tabbatar da nasarar da ‘ya’yanta kuma gwamnonin Legas, Ebonyi Kuros Riba suka samu a zaben 2023 da ya gabata.

Morka ya ce duk da dai APC ta fadi a shari’ar  Kano, Zamfara, Bauchi da Filato, hakan ba zai hana jam’iyyarsu ta APC yin na’am da sakamakon shari’un ba.

“Muna taya gwamnonin da suka yi nasara musamman gwamnoninmu da suka hada da Babajide Sanwo-Olu na Legas da Francis Nwifuru na Ebonyi da kuma Bassey Out Jihar Kuros Riba.

“Muna yi musu fatan alheri yayin da suke ci gaba da yi wa jihohinsu da kasa baki daya hidima. Kuma muna kira gare su da su ba da himma tare da wanzar da zaman lafiya,” in ji APC.