AFCON: Nijeriya ta kira Terem Moffi don maye gurbin Victor Boniface

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An gayyaci dan wasan Nice Terem Moffi a gasar kofin Afrika da za a fara a karshen mako mai zuwa a maimakon Victor Boniface da ya ji rauni, inji Super Eagles a ranar Talata.

Wannan koma-baya ne ga Super Eagles, wadda ta ke fatan daukar kofin babbar gasar qwallon kafa ta Afirka karo na hudu.

Mai shekara 23, shi ne na baya-bayan nan da ya ji rauni a tawagar Nijeriya da ta ke cikin wadanda za su fafata a gasar da za a fara ranar 13 ga watan Janairu a Abidjan.

An kira dan kwallon Nice, Terem Moffi, domin maye gurbin Boniface, yayin da ake jiran amincewar hukumar kwallon kafar Afirka da kuma kungiyar da ke buga Ligue 1.

Boniface ya shiga jerin ‘yan wasan Nijeriya da suka hakura da buga Afcon a bana, sakamakon rauni da suka hada da mai taka leda a Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi, da na Leicester City, Wilfred Ndidi.

Sai dai ana sa ran Kelechi Iheanacho, mai taka leda a Leicester City wanda bai samu halartar sansanin Super Eagles ba, zai je sansanin tawagar kafin ta nufi Ivory Coast.

Boniface yana kan ganiya a kungiyar Jamus, wanda ya ci kwallo 10 ya kuma bayar da bakwai aka zura a raga a Bundesliga a kakar nan.

Nijeriya tana rukunin farko a gasar Kofin Afirka da za ta fara wasa ranar 14 ga watan Janairu.

Haka kuma Super Eagles za ta fuskanci mai masukin baki Ivory Coast da kuma Guinea-Bissau a dai rukunin farkon.

Moffi ya fara buga wasansa na farko a duniya a watan Yunin 2021, inda ya zura kwallaye hudu a wasanni 14, amma da farko ya kasa samun nasara a kungiyar kocin kungiyar Jose Peseiro duk da kwallaye shida da ya ci wa Nice tun farkon kakar wasa ta bana.

Dan wasan mai shekaru 24, zai buga gasar kofin Afrika na farko tare da dan wasan Napoli Victor Osimhen.

Nijeriya dai tana rukunin A ne da mai masaukin baki Ivory Coast, Guinea-Bissau da Equatorial Guinea, wadanda za su kara da juna ranar 14 ga watan Janairu a Abidjan.