Zan tabbatar da bai wa duniya labarin Nijeriya da Afirka – Shugaban Muryar Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Muryar Nijeriya, Mallam Jibrin Baba Ndace, ya ce hukumar za ta hada kai da masu ruwa da tsaki wajen bai wa duniya labaran Nijeriya da Afirka.

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya jagoranci ma’aikatan hukumar a ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar Media Trust da ke Abuja.

Yayin da ya bayyana Nijeriya a matsayin kasar da ba ta cika dari bisa dari, ya ce akwai labarai masu kyau da yawa da za a fada game da Nijeriya.

“A Muryar Nijeriya abin da nake yi tun lokacin da na hau karagar mulki shi ne na kai ziyara, a matsayinmu na masu yada labarai, a shirye muke mu hada kai da ’yan Nijeriya da masu ruwa da tsaki don ba da labarin Nijeriya da Afirka.

Malam Ndace ya ce, aikinsa na babban darakta na Muryar Nijeriya yana tafiya ne daidai da irin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna wajen tafiyar da al’amura.