Gwamnan Kebbi ya rantsar da Alƙalin-alƙalai da shugabannin wasu hukumomi 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi 

Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr Nasir Idris Kauran Gwandu ya rantsar da Mai shari’a Umar Abubakar a matsayin babban alqali da Khadi Sadiq Usman Mukhtar a matsayin Grand Khadi na jihar.

Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ne ya kaddamar da bikin rantsarwar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Birnin Kebbi a ranar Litinin.

Da yake gabatar da mutanen biyu ga gwamnan domin rantsar da shi, sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida ya kuma karanta sunayen shugabanni da mambobin hukumar da Parastatals da za a kaddamar.

Bayan rantsuwar, Gwamna Nasir ya kuma kaddamar da hukumomin gudanarwa na manyan makarantu guda shida da kuma wasu hukumomi uku.

A jawabinsa a wajen bikin, Gwamna Malam Nasir Idris, ya bayyana jin dadinsa da bikin inda ya bayyana shi a matsayin mai tarihi.

Ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da adalci ga daukacin al’ummar.