Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Nasarawa

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa da ke gabanta.

Kotu ta yi hakan ne a zaman ci gaba da sharilar da ta yi a wannan talatar.

Ta ce za ta sanar da bangarorin da shari’ar ta shafa ranar da za raba gardama idan ta tsayar da rana nan gaba.

Ana fafata shari’ar ne tsakanin Gwannan jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma Jam’iyyar PDP a jihar tare da dan takararta na gwamna, David Ombugadu