‘A Tribe Called Judah’: Fim ɗin Nollywood da ya yi fito-na-fito da Hollywood 

Daga AISHA ASAS

Idan a na maganar masana’antar finafinai da ta yi wa kowacce masana’anta irinta zarra ta fuskar shahara, kwarewa, da kuma samun cigaba, to tabbas masana’antar finafinai ta Turai, wato Hollywood ce za a ambata. Dalilin kenan da suka fi kowacce masan’antar fim samar da kudaden shiga, wanda ya sa jarumai da ma’aikatansu suka zama mafi arziki daga cikim masu aikin fim na duniya bakidaya.

A vangaren amfanar da kasa kuwa, Hollywood na daya daga cikin wuraren da kasar ke amfana da su, sakamakon yawan mutanen da ke da ra’ayin kallon su, dalilin bajinta da kwarewa da suke nuna wa a finafinai, tare kuma da amfani da kayan aiki masu kyau, wanda hakan ke sa su narkar da kudi a kowanne fim idan suka yi shi. Sai dai hakan bai cika zama matsala gare su ba sandiyar samun damar mayar da abinda suka kashe har ma da riba mai tarin yawa.

Shafin Nishadi na jaridar Blueprint Manhaja na wannan makon zai yi tsokaci kan sharaharren fim din nan da ya kafa tarihi a masana’antar finafinai ta Nijeriya ko ma ince ta Afrika bakidaya, wato ‘A Tribe Called Judah’, ta hanyar zama fim irinsa na farko a Nijeriya da ya tava tara zunzurutun kudi har biliyan daya a sinima ta cikin gida, wanda ya ba shi damar gogayya da fitattun finafinai da suka samu karvuwa a duniya.

Kafin mu tsunduma ga batun da ya shafi wannan kayataccen shiri, zan so mu yi wa junanmu tambayar, shin me ya sa ba a yi ba sai bana? Me ya sa masana’antar fim ta Nijeriya ba ta tava taka wannan tsauni ba duk da baiwa da fiqira da Allah Ya azurta kasar tamu da ita? Me ya sa finafinan namu ba su yi tasiri ba a duniya kamar yadda wakokinmu suka yi ba?

Duk da ban kasance gwana ko kwararra a harkar fim ba, sai dai dan binciken da na yi ya tabbatar ba mu rasa baiwar samar da finafinai masu ma’ana ba kamar sauran kasashe ba, asalima bincike ya nuna babu inda aka fi samun mutane masu baiwar rubutu kamar Afrika.

Manyan matsalolin da su ka yi wa finafinan mu dabaibayi suka hana su isa inda ya kamata su isa su ne, rashin daukar ‘kasada’, da kuma bijirewa fahimtar ita kanta sana’ar ta fim, da kuma rashin neman kwarewa a cikin ta.

Lokuta da dama mun fi mayar da hankali kan fitar da fim fiye da yadda duniya za ta kalle shi, kuma mukan saka tsoron faduwa a cikin sa don haka muke taka-tsan-tsan kan kudaden da za mu kashe a wurin yin sa don kallon za mu iya hasara a karshe. Kenan ba mu dauki harkar ta fim sana’a babba ba, dalilin kenan da ba kasafai ka ke ganin manyan masu kudi sun saka jari a harkar ba, ko kuma su sun mallaki kamfanin yin fim ba, saboda ana kallon ta a matsayin ‘yar karamar sana’a.

Wannan ne ya sa, babu kayan aiki da ke tafiya tare da zamani a wurin mu, saboda kaya ne da ke bukatar makudan kudade, sannan babu wadatattun kudaden da za su bayar da ilimin harkar mai yawa ga wadanda ke yin ta, domin ba za a iya daukar nauyin jarumai ko masu aiki zuwa wasu kasashe don kwaso cigaban da aka samu a harkar ba. Iya wadannan kawai za su iya zama silar da muke tsallake namu finafinai mu je ga kallon na wasu kasashen. 

Akwai kuma sha’ani na gaggawa wadda wani lokacin sha’anin kudi ke dauke da alhakin ta. A wani dan karamin bincike da na yi ‘yan shekarun baya, na lura da daya daga cikin ababen da ya sa finafinan kasashen waje yi wa namu zarra akwai hakuri, domin za a iya daukar tsayin shekaru biyu ana daukar shirin fim guda daya tilo.

Me karatu zai iya tambayar yadda shirin fim guda ba kuma mai dogon zango ba zai iya daukar shekaru biyu ana daukar shi, wato dai me suke yi kan abinda za su iya gamawa a wata biyu zuwa uku?

Zan iya fara amsa wannan tambaya da tambaya, yayin da ka ke kallon finafinai musamman na Turawa, shin ba ka cika samun shagala har ka manta da cewa abinda jarumin ke yi ba ainayin rayuwarsa ba ce a zahiri?

Bari na bada misali da wasu rol kamar na likita, lauya da kuma aikin kaki. Idan kana kallon fim da ya shafi zuwa asibiti, za ka tarar da likitin cikin fim din na magana da bayanin cuta ko maganin ta tamkar da gaske likitan ne, kuma lokuta da dama idan za ka koma ka yi bincike za ka tarar cutar ko bayanin da ya yi daidai yake a ilimance.

Duk da cewa akwai ‘khala’iyya’ a ciki, za ka samu mafi yawan curutan da ake magana kansu na hakika ne, da kuma alamomin su ko hanyar samuwar su.

Ko a kotu, za ka samu ana fadar dokokin da idan ka je bincike za ka tarar da vangaren su ba wasan kwaikwayo ba ne. ko kuma idan ana maganar fim na fada, wato ‘action film’ a turance, yanayin yadda suke riqe bindiga, yadda suke fada, da sauran ababen da ya shafi bangaren za ka tarar tamkar a zahiri.

Abin tambaya a nan, ya ake iya samun wannan kwarewa a tattare da jaruman ko ince ilimin abinda ba nasu ba?

Bincike ya tabbatar da a duk lokacin da za a yi shirin fim ire-iren wadannan, to fa akan dauko kwararre a vangaren na gaske, shi zai koya bangaren ga jaruman, tare da gyara duk wani kure da za su yi na baki da na aikace, kuma ba za a dauki shirin ba har sai an tabbatar jaruman sun samu yin basaja daga rayuwarsu zuwa irin rayuwar da ake son su yi a fim din. Anan kuwa zancen kudi ya kara zuwa.

Da a ce za a wayi gari mutane irin Dangote za su nuna sha’awa ga sana’ar fim, kuma su shirya yin ta don samun kudi na gaske, da tabbas za a iya samar da finafinai da za su iya shiga jerin finafinan da duniya za ta yi amo da kwarewar su, domin an ba mu iyawa, hanyoyin amfani da ita ne kawai babu.

Abu na qarshe bincike ya nuna akwai rashin daukar sana’ar ita kanta da sahihiyyar ma’anar da take da iya, wato hanyar samun kudi, ba matakan takawa na kai ga samun kudi ba.

Ma’ana yin fim don samun shuhura da za a yi amfani da iya wurin samun kudi.
Wannan ba iya masana’antar finafinai ta Arewa wannan matsala ta tsaya ba, kamar yadda wasu ke gani.

Matsala ce da kusan duk wata masana’anta da ke shirya fim a fadin Nijeriya tana da iya. Duk da cewa wasu na kafa hujja da irin tauyewar da masu shirya fim ke masu ta bangaren biyan kudi, wato jaki da shan duka……, wanda zai iya sa sai ka amshi aiki goma ko ashirin a shekara a kokarin samun abinda zai iya rike ka, savanin sauran kasashen da suka cigaba, jarumi zai iya samun kudaden da za su iya rike shi tsayin shekaru a fim daya, ta dalilin tsarin lasan romon fim da suke da shi, wato jarumi zai dinga samun kaso daga yadda fim din da ya fito ciki ya yi tashe. 

Idan fim ya fita, duk wata riba da fim din zai samu jarumin ciki na da kaso daidai da yadda yarjejeniyar tasu ta tanada, wanda hakan na ɗaya daga cikin dalilan da ke karawa jaruman kwarin gwiwa, sanin idan ba ka yi namijin kokari ba akwai yiwar fim din ya ki karbuwa, hakan na nufin rashin samun kudade a aljihunka masu nauyi.

Kasancewar darasin namu ba ya karkata kawai kan wannan dogon zance da muke yi ba, wanda hakan na nufin dasa aya don fuskantar maudu’in namu. Shin me wannan fim ya kunsa da ya sa ya bambanta da sauran takwarorinsa?