Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan shari’ar zaɓen gwamnan Kebbi

Kotun Ƙoli ta keɓe yanke hukunci kan karar da aka dauka ta neman a sauke Dr Nasir Idris na jam’iyyar APC a matsayin Gwamnan Jihar Kebbi.

Kotun ta dauki wannan matsaya yayin zaman ci gaba da sauraren shari’ar da ta yi ranar Talata karkashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, bayan ta karrbi bayanan lauyoyin duka bangarorin.

Kotun ta ce za ta sanar da bangarorin da lamarin ya shafa baya ta tsayar da lokacin da za ta yanke hukunci kan shari’ar.

Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi da dan takarar gwamnanta a zaben 2023, Manjo Janar Aminu Bande, su ne suka daukaka kara suna neman kotu da sauke nasarar da Nasir Idrin ya samu a zaben.