Kotun Ƙoli: Zamfarawa sun yi fitar farin dango don taya Gwamna Lawal murna

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin da ta gabata dubban Zamfarawa cike murna suka yi dandazo a Gusau, babban birnin jihar domin tarbar Gwamna Dauda Lawal in Gusau, bayan dawowa daga Kotun Ƙoli.

A ranar Juma’ar da ta gabata Kotun Ƙoli mai zamanta a Abuja ta tabbatar  da Gwamna Lawal a matsayin wanda ya lashe zabe Gwamnan Zamfara, tare da yin watsi da karar da bangare hamayya ya daukaka na kalubalantar nasarar tasa.

Cikin sanarwar manema labarai da ya fitar, Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce masoyan gwamnan sun yi fitar farin dango don nuna farin cikinsu dangane da nasarar da Lawal ya samu a kotu.

Ya ce, “Hanyoyin sun cika da jama’a kuma cike da farin ciki inda suke ta daga wa Gwamna hannu yayin da tawagar motoci gwamna ta ratsa ta tsakiyar gari.

“Gwamnan ya kasance cikin motarsa da ake kira Bazamfara, inda shi ma ya leko yana daga wa masoyansa hannu yayin da yake wucewa ta Karamar Hukumar Tsafe, Kwatarkwashi da Damba zuwa dandalin ‘Freedom Square’  da ke Gusau, babban binin jihar.”

Ya kara da cewa, an safe sa’o’i 10 ana gudanar da wannan taro na taya murna ga Gwamna Lawal.

Sa’ilin da yake jawabi ga dandazon masoyansa a danalin Freedom Square, Gwamna  Lawal ya ce, “Hukuncin da Kotun Koli ta yanke ya kara mana kwarin gwiwa game da fannin shari’a.

“Ina godiya ga fannin shari’a da Gwamnatin Tarayya na rashin tsoma baki a shari’ar. Hakan ya karfafa gwiwar daukacin ‘yan kasa.

“Ina ba ku tabbacin tsaro shi ne bangaren da muka fi bai wa muhimmanci kamar yadda na yi alkawari. Za mu ci gaba da kokarin ganin bayan matsalolin tsaro.

“Haka nan, mun samu ci gaba a bangarorin harkar noma da lafiya da tattalin arziki da sauran muhimman fannoni.”

Lawal ya kara da cewa, a can baya gwamnatin da ta shude ta haramta musu wuri don gudanar da taron siyasa duk kuwa da cewa sun cika dukkan sharuddan da doka ta shimfida, wanda hakan ya sa suka shirya taron a wannan dandalin da suka hadu. Don haka ya, “Wannan ya sa muka sauya wa dandalin suna suna zuwa Dandalin ‘Yanci (Freedom Square).”