Buni ya samar da romon dimukraɗiyya a Nengere – Hon. Yerima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Karamar Hukumar Nengere a Jihar Yobe, Hon. Salisu Yerima ya bayyana irin kokarin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi wajen samar da romon dimukradiyya ga al’ummar yankin tun bayan hawansa mulkin jihar a 2019.

Hon. Yerima ya ce Gwamna Buni ya yi abin a yaba da irin jagorancinsa na cire kyashi wajen dorawa daga inda tsohon gwamnan jihar, kuma Ministan Harkokin ‘Yan Sanda na yanzu, Sanata Ibrahim Geidam ya tsaya.

Ya ce an samu nasarori masu tarin yawa da suka haifar wa jihar da mai ido, inda ya ce shirye-shiryen gwamnan sun hada da karfafa wa masu karamin karfi da gidajen marayu, aikin yi ga matasa.

Hon. Salisu Yerima ya ce Gwamna Buni ya samar da ayyukan more rayuwa a karamar hukumar ta Nangere da suka hada da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a cikin birane da kauyuka da gyare-gyaren rijiyoyin burtsatse da sauran kananan hukumomi 17 na jihar a karkashin fatan sabuntawa.

“Samar da ingantaccen ilimi a matakin firamare da sakandare da gyaran makarantu a birni da karkara da samar da kujerun firamare da kwararrun malamai masu shaidar digiri da NCE.

“Bangaren tsaro kuwa, mun sayo motoci da na’urorin tsaro ga jami’an tsaro don tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin ganawa akai-akai da shugabannin tsaro na karamar hukumar Nangere da suka hada da ‘yan sanda, sojoji, ‘yan banga da sauran masu ruwa da tsaki irinsu hakimai, shugabannin addinai da shugabannin al’umma. Kana kuma a kullum muna miqa rahotonmu ga maigirma Gwamna Mai Mala Buni.”

Hon. Salisu Yarima ya kuma yi kira ga matasan karamar hukumar Nangere da su rika mutunta kundin tsarin mulki da kuma girmama dattawa a yankinsu kasancewar su shugabanni gobe, wanda hakan zai sa su zama shugabanni nagari. Kana ya horesu da su guje wa tu’ammali da miyagun kwayoyi  kwayoyi.

Haka zalika ya bayyana farin cikinsu da kafa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas da tsohon Shugaban Kasa Muhammad Buhari da yi wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal ya yi ruwa ya yi tsaki a zauren majalisar dattawa domin kafa hukumar ta NEDC wanda a cewarsa an samu cigaba sosai, inda hukumar ta samar da ayyuka yin ga matasan yankin bangaren tsaftace birni da kauyuka wanda Maigirma Gwamna Mai Mala Buni ya samar da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.