Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Kwamandan hukumar dake yaki da sha tare da safarar miyagun kwayoyi na kasa reshen jihar Nasarawa Peter Onche-Odaudu ya bukaci al’ummar jihar Nasarawa baki daya musamman sarakunan gargajiya su ruka hada kai da hukumar a jihar ta Nasarawa don ci gaba da yaki da masu laifin sha tare da safarar miyagun kwayoyi a jihar da kasa bakidaya.
Peter Onche-Odaudu ya yi kiran na musamman ne ta wani sakon sabuwar shekarar 2024 na musamman dauke da sanya hannunsa da aka bai wa wakilinmu kwafi a ofishin hukumar dake birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar ranar Talata 9 ga watan Janairun shekarar 2024 da ake ciki.
Kwamanda Peter Onche-Odaudu ya bayyana cewa ya zame wa hukumarsa dole ne ta yi wannan kira a kokari da ta ke yi don ci gaba da rage ko kawo qarshen ayyukan masu safara da shan muggan qwayoyi a fadin jihar bakidaya musamman a yanzu da aka shiga sabuwar shekarar 2024.
Ya ce ba shakka duk da hukumar ta samu hadin kai da goyon baya tsakanin al’ummar jihar musamman shugabannin addinai da sauran jama’a a yayin gudanar da ayyukan ta a jihar a shekaru da suka gabata dole ne ta sake nanata kiran a wannan sabuwar shekara da aka shiga don bai wa hukumar damar cigaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na dakile ayyukan ‘yan bata-garin a fadin jihar baki daya.
Ya yi amfani da damar inda ya taya al’ummar jihar ta Nasarawa baki daya murnar zagayowar sabuwar shekara ta 2024 inda ya nanata cewa dole ne a samu hadin kai da kyakkyawar dangantaka tsakanin su da hukumar don cimma burin a karshe.
Har ila yau kwamanda Peter Onche-Odaudu ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga shugabannin al’umma a duka matakai musamman iyayen yara su tabbatar suna ci gaba da bai wa ‘ya’yan su kyakkyawar tarbiyya a sabuwar shekarar nan musamman dangane sha tareda safarar miyagun kwayoyi don acewar sa hukumar tasa bazata yi sannin gwiwa ba wajen cigaba da gudanar da sintiri tare da cafke masu aikata ire-iren laifuffukan na shan muggan kwayoyin tare da yin safararsu a fadin jihar baki daya inda ya gargadi masu niyaya.
