Yadda Muhammad Rili ya farfaɗo da darajar hukumar KADA a Kaduna

Daga SANI SHEHU LERE a Kaduna

Sau da yawa mutane kan zabi hukumomin da inda so samu ne a kai su don yin aiki, ba don komai ba, sai don irin maikon da ake hange a cikinsu da saukin aiki.

Zuwan Hon. Muhammada Rili Hukumar KADA, ta isa ta canza wa mutane irin wannan tunani, su gane cewa a she kowane ofishi na da irin nasa gwargwadon maikon amma sai in an samu mutumin da ya iya murza gabobin da maikon da zai iya fita. Ma’ana, mutum ke gyara ofis, ba ofis ne ke gyara mutum ba.

A kasa da ‘yan watanni 6, Hon. Muhammad Rili ya yayyafa wa Hukumar KADA ruwa har ta farka daga dogon sumar da ta tsinci kanta a ciki tsawon zamani da wasu wadanda iya kokarinsu bata dara abin da suka iya yi ba, da kuma halin da suka barta.

Akwai hukumomi da cibiyoyi masu tarin yawa kuma tsoffi ba sabbi ba a Jihar Kaduna, wadanda sam-sam ba a san su ba, ko sanin tasirinsu ba a aikace sai dai a takardu, to Hukumar KADA na ciki.

Domin kuwa tsawon zamani wannan hukumar na nan tun lokacin da ake kiranta  (KADP) kafin daga bisani Malam Nasiru El-Rufa’i ya maishe ta (KADA) ana kuma ware mata kaso daga asusun gwamnatin jiha, ban da dinbin tallafin da take karva daga Hukumar Ayyukan Aikin Gona ta Kasa, da Asusun bada tallafin samar da abinci da kungiyoyin kasashen ketare, amma al’umma sam ba su ganin tasirinta sai a zahiri sai dai a takardu.

Zuwan Hon. Muhammad Rili a kasa da watanni shida kacal, ya sauya fasalin ma’aikatan ya daga darajarta har ta zama a yanzu babu wata cibiya da al’umma ke iya jin bugun numfashinta tun daga nesa sai KADA.

A yanzu ita ce ma’aikatar da al’umma ke tururuwan zuwa a kullum rana don neman dacewa da irin alhairan da ke tattare da ofishin da suka hada da: Samar da tallafin noman alkama; Tallafin noman shinkafa; Tallafin noman masara; Bada tallafi da horas da manoman kaji da kifi da sauran dangin tsuntsaye; Bada tallafi da horas da makiyaya shanu da awaki da dai sauransu.

Baya ga wadannan, Rili a yanzu haka ya bada kwangilar gyara ofisoshin ma’aikatar da sauya fasalinta daga tsohon yayi, zuwa na zamani, tare da samar da kayayyakin ofis na zamani kamar na’urar sanyaya daki da dukkan abubuwan da ofis ke bukata, don jin dadi da walwalar ma’aikatan.

Ana sa ran gwamnatin Jihar Kaduna za ta zama ta daya a fadin Nijeriya ta fuskar samar da abinci da naman dabbobi, saboda ingantuwar wannan ma’aikatar da take aiki kaitsaye da manya da matsakaita da kuma kananan manoma don wadata kasa da abinci.