Aminin Pantami ya ba da tallafin N50m don kuɓutar da ‘yan matan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Abuja

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Minista kuma fitaccen malamin Islama, Farfesa Isa Pantami, ya sanar cewa an tara kudi Nairia miliyan 50 domin ceto da ‘yan matan zuri’ar Al-Kadriyar da ‘yan binbdiga suka yi garkuwa da su a yankin Abuja.

Pantami ya ce wani amininsa ne ya ba da tallafin ragowar Naira miliyan 50 daga cikin miliyan 60 da ‘yan bindigar suka bukaci a biya, bayan da ya tattauna batun da shi.

A cewar tsohon ministan, “Alhamdu lil Laah! A kashin kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga barayi. Amma tun da a bayyane yake mun rasa ‘yarmu Nabeeha jiya, sannan ana yi wa ragowar biyar din da ke hannusu barazana kamar yadda mahaifi ya shaida mini jiya da yau.

“Bugu da kari, na zanta da wani aminina kuma dan’uwa wanda ya amince ya biya ragowar Naira miliyan 50 daga cikin miliyan 60 nan take.

“Na tura wa aminin nawa lambar akawunt din mahaifin yaran, Mansoor Al-Kadriyar, don ya tura kudin kai-tsaye. Duk karin da aka samu daga jiya uban zai yi amfani da shi wajen kula da lafiyar yaran in sha Allah.”

Kazazlika, Pantami ya yi addu’ar Allah Ya saka dukkan wadanda suka tallafa wajen ganin an ceto wadannan yara, ya kuma yi wa bangaren tsaron kasa fatan samun nasara wajen yaki da matsalolin tsaro.

A ranar Talatar da ta gabata ‘yan bindiga suka kai samame yankin Bwari a Abuja inda suka yi awon gaba da wani magidanci tare da ‘ya’yansa mata su shida.

Daga bisani aka sako mahaifin inda ‘yan bindigar suka bukaci ya je ya kawo musu kudi Naira miliyan 60 kafin su sakar masa ‘ya’yansa.