Dole ne a ɗore da ya ƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya

Ranar Alhamis din da ya gabata ne al’ummar duniya suka ware a matsayin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya. Majalisar Dinkin Duniya ta kuduri mai lamba 58/4 na ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2003 ta ware ranar na kowace shekara a matsayin ranar wayar da kan jama’a game da laifukan da ke kawo cikas ga cigaba da kuma talauta jama’a.

Har ila yau, rana ce ga shugabannin siyasa, gwamnatoci, hukumomin shari’a, kungiyoyin fafutuka da kungiyoyin farar hula don sabunta alkawurran da suka dauka na kawar da wannan abu da aka gano a matsayin wani lamari mai sarkakiya na zamantakewa da siyasa da tattalin arziki wanda ya shafi dukkan kasashe.

Taken bikin na bana shi ne ‘Hakkinku, Matsayinku: Ku Yi Bara’a ga Cin Hanci da Rashawa.’ Tana neman ganin wadanda laifin ya shafa su mai da hankali kan wannan barazana a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a duk inda aka samu gindin zama.

Kimanin shekaru 15 bayan kaddamar da taron wayar da kan jama’a na shekara-shekara, sabuwar kididdigar cin hanci da rashawa ta nuna har yanzu yawancin kasashen duniya ba su samun cigaba ko kadan a yakin da ake yi da cin hanci da tashawa a duniya.

Haqiqa, an san cin hanci da rashawa a matsayin cuta mai saurin yaduwa da ke addabar kasashen duniya daban-daban. Yana iya ruguza kowace al’umma, ya hana ci gabanta, da gurgunta mulkin dimokuradiyya, ya haifar da gwamnatoci marasa inganci, da kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kawo cikas ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Wannan dodo yana bayyana ta hanyoyi daban-daban kamar, cin hanci da rashawa, rashin aiki da ilimi da wawure dukiyar jama’a.

Babu wata kasa guda da ke samun tsaftataccen lissafi na lamarin kamar kasashen da aka ware a matsayin masu tasowa da marasa ci gaba sun duk fi fama da matsalar. Nijeriya ta yi fama da matsalar cin hanci da rashawa a cikin shekaru daya da rabi da suka wuce. Ta kasance ta 143 a shekara ta 2011, ta 139 a shekarar 2012 da ta 144 a shekarar 2013. Kamar yadda yake a shekaru hudu da suka gabata, tana matsayi na 136 daga cikin qasashe 175, a cewar kididdigar cin hanci da rashawa ta ‘Transparency International’ (TI).

Denmark har yanzu tana rike da matsayi na farko a matsayin kasa mafi karancin cin hanci da rashawa a duniya daga cikin kasashe 175 da TI ta bincika. Botswana ita ma ta rike matsayinta na farko a matsayin kasa mafi karancin cin hanci da rashawa a Afirka kuma ta 31 a duniya. A kimantawar shekarar 2017 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta yi, Nijeriya ce kasa ta 148 a cikin kasashe 175 mafi karancin cin hanci da rashawa.

Da dama daga cikin masu sa ido kan cin hanci da rashawa a ciki da wajen kasar nan sun danganta nasarar da Nijeriya ta samu a yakin da ake yi da dodanniya da sabon karfin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa yakin tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 2015. Amma yakin bai yi nisa ba duk da cewa an samu nasara a samuwar wasu gabobin yaki da rashawa da kuma matakan da aka sanya don yakarsa.

A baya-bayan nan dai cin hanci da rashawa ya kaurace wa katutu saboda wadanda ke rike da madafun iko sun nuna rashin kishin kasa wajen baiwa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata musamman a gwamnatin da ta shude. Lamarin da ya zama dole hukumomi su karbi takardar ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kafin a gurfanar da wasu masu cin hanci da rashawa a gaban kuliya domin shari’a, ya sa abin ke ta tafiyar katantanwa.

Duk gwamnatin ta himmatu wajen ganin ta kawar da cin hanci da rashawa a rayuwarmu ta kasa, dole ne ta baiwa hukumomin damar aiwatar da aikinsu na yakin.

Wani abin lura kuma shi ne wani manufar da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi. Dabarar ta haifar da sakamako mai kyau kafin a daga baya kuma a yishuru da batun.

Kasashe da dama a fadin duniya sun dauki tsauraran matakai don dakile barazanar. Misali Chana ta zartar da hukuncin kisa ga wadanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa. Wani abin mamaki shi ne wasu manyan ‘yan Nijeriya sun ba da shawarar a yi wa Nijeriya irin wannan doka.

Nijeriya ta yi qaurin suna a wajen cin hanci da rashawa a duniya, lamarin da yake daqushe kima da martabar kasar a idon sauran manyan kasashe.

A baya, wani lokaci yayin taro a kan yaki da rashawa a duniya, an ambato tsohon firaministan Birtaniya, David Cameron na cewa ‘Nijeriya kasa ce da ta gawurta wajen cin hanci da rashawa’.

Ko a alkaluman ayyukan rashawa na shekara-shekara, da kungiyar Transparency International ke fitarwa, Nijeriya na gaba-gaba a duniya cikin jerin kasashen da cin hanci ya yi wa katutu.

Masu rike da mukaman siyasar Nijeriya, na cikin wadanda ake zargi da goya wa cin hanci da rashawa baya a kasar.

Saboda da zarar mutum ya samu wata kujerar gwamnati, cikin dan kankanin lokaci za a ga rayuwarsa ta canja saboda irin handama da babakere da kuma almundahanar da ake zargin su ne dalilan da ke sanya su yin rayuwar fiye da albashin da suke dauka.

A cikin ‘yan kwanankin nan, akwai wasu manyan ‘yan siyasa mata da suka rasa kujerunsu na gwamnati saboda zargin sun tafka rashawa, inda gwamnati ta dakatar da su domin gudanar da bincike a kan lamarin.

A makon da ya gabata, an fara da dakatar da shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta kasa NSIPA, Halima Shehu, sai kuma a ranar Litinin, aka dakatar da ministar ta jinkai da yaki da talauci, Betta Edu.

Ya kamata gwamnatin Shugaba Tinubu ta cigaba da yin amfani da ra’ayin mafi yawan ’yan Nijeriya tare da cigaba da yaki da cin hanci da rashawa ba tare da la’akari da sanwar sa ba har sai an durkusar da dodon, hakan zai samu ta hanyar karfafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawada kuma hanzarta shari’ar cin hanci da rashawa da ke addabar kotunan mu da kuma kara kaimi wajen kwato kadara. Cin hanci da rashawa sun fi ‘yan bindiga muni. Kamar yadda marigayi tsohon shugaban Ghana Jerry Rawlings ya tava furtawa, “’Yan bindiga suna satar mutane amma masu cin hanci da rashawa suna satar al’umma ne.”

Mummunan laifukan da ke talauta talakawa da kuma kawo cikas ga cigaba dole ne a magance shi tare da duk abin da ya cancanta. Hukuncin da wasu manyan ma’aikatan gwamnati, da masu rike da mukaman siyasa suka yi ya zama kyakkyawan cigaba.

Ya kamata hukumomin yaqi da cin hanci da rashawa su cigaba da gudanar da ayyukansu. Yaki da cin hanci da rashawa wani aiki ne da ya kamata mu goyi baya idan har ana son cigaban kasa, in ba haka ba, za mu rasa makomarmu gabadaya.