Yadda za ki kula da fatarki a lokacin sanyi (3)

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, mun kawo yadda za ki iya kula da fatarki, da kuma dabi’un da ya kamata mu dinga yi a lokacin sanyi. A yau za mu tabo wani bangare da ke bukatar kulawa a lokacin sanyi, wato kafa da kuma gashi.

A lokacin sanyi ba iya fata ke shiga yanayi ba, asali ma ga wasu kafa ta fi shiga mawuyacin hali fiye da sauran fatar jiki.

Kafa wata muhimmiyar vangare ce a jikin mutum da ya kamata a ba ta kulawa ta musamman a lokacin sanyi.

Ta yaya za a iya kula da kafa a lokacin sanyi?

Za ki iya amfani da hanya mai sauki wurin kula da kafa ta hanyar amfani da gishiri, ruwan kal (vinegar), da kuma ruwan zafi.

Za a sanu roba, a zuba ruwan zafi daidai da yadda kafar za ta iya dauka, a zuba ruwan kal da kuma dan gishiri, sannan a saka kafar a ciki, har tsayin lokacin da ruwan za su huce, sannan a yi amfani da dutsin goge kafa a goge kafar har sai duk wata mataciyyar fata ta fita.

Sai a samu mai kamar man kade ko makamantan sa, a shafe kafar da shi. Kuma a tabbatar da ba a bar ta ba mai ba.

Domin daya daga cikin ababen da ke kara matsalar akwai bushewa, kuma mai zai iya magance ta.

Sannan yana da kyau mu kula da suturce kafar, ba wai kawai don jin sanyi ba, sai don ba wa kafar kariya. Kuma hanya ce da za a rage mata saurin bushewa bayan an shafa mata mai.