Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu ya isa Owerri don rantsar da Gwamna Hope Uzodinma wa’adi na biyu

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

A halin da ake ciki, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya isa Owerri, babban birnin Jihar Imo domin shaida bikin rantsar da Gwamna Hope Uzodinma a wa’adin mulkin jihar na biyu.

MANHAJA ta kalato cewa, Tinubu ya bar Abuja zuwa Imo ne jim kadan bayan bikin Ranar Tunawa da Sojoji.

Bikin rantsarwar na guna ne a babban filin wasannin motsa jiki na Dan Anyiam da ke Owerri.

Yayin ziyarar, ana sa ran Shugaba Tinunu zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar.

By Editor