‘Yan bindiga sun kashe ƙarin mutum 3 daga cikin 10 da suka sace a Abuja

Spread the love

*Sun ƙara kuɗin fansa zuwa N700m

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu mutum 10 a yankin Dutse, Abuja a ranar 7 ga Janairun da ake ciki, sun kashe karin mutum uku daga cikin mutane 10 da suka yi garkuwa da su.

Majiyarmu ta ruwaito cewar, ‘yan bindigar sun aikata hakan ne a matsayin gargadi ga ‘yan wadanda ke hannunsu kan kudin fansar da suka nema a biya.

A cewar majiyar, ‘yan bindigar sun kara kudin fansar zuwa Naira miliyan 100 kan kowane mutum sabanin Naira miliyan N60 da suka nema da farko.

Da wannan, ‘yan bindigar na neman a biya su miliyan N700 kan ragowar mutum bakwai da ke hannunsu.

Mazauna yankin sun ce ana zargin ‘yan bindigar sun kashe karin mutum uku din ne saboda jinkirin biyan kudaden da suka bukata.

Bayanai sun ce barayin sun zuba gawarwakin mutum hudun da suka kashe a kusa da mararrabar Idah a hanyar Bwari-Jere cikin yankin Karamar Hukunmar Kagarko, Jihar Kaduna.

Daga cikin gawarwakin har da ta Nabeeha Al-kadriyar, wadda daliba ce a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

By Editor