Ɓata-gari sun kai hari asibiti sun yi awon gaba da gawa a Ekiti

Daga BASHIR ISAH

Wasu bata-garin matasa a Jihar Ekiti sun kai hari Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar (EKSUTH) da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar inda suka sace wata gawa.

MANHAJA ta kalato cewar wannan al’amari ya auku ne a ranar Litinin lamarin da ya haifar da tsaiko a ayyukan asibitin.

Bayanai sun ce, gawar da aka sace din ta mahaifin daya daga cikin bata-garin ne. Sai dai, babbu cikakken bayani kan dalilin da ya sa matasan daukar wannan mataki.

Faruwar wannan al’amari ya sanya kungiyar likitoci a jihar ta bai wa mambobinta umarnin fara yajin aikin sai-baba-ta-gani domin nuna rashin jin dadinta kan abin da bata-garin suka aikata wa mambobinta a asibitin da lamarin ya shafa.

Kazalika, an ce maharan sun lalata wasu kayayyakin aiki bayan da suka shiga harabar asibitin.

Umarnin shiga yajin aikin na kunshe ne cikin wasikar da kungiyar ta aike wa shugaban asibitin, Farfesa Kayode Olabanji kuma mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Dr Famous Adeyemi.