Messi ya lashe kambun “Gwarzon Ɗan Wasan” shekara na FIFA

A karo na uku, shararren dan wasan kwallon kafar nan, Lionel Messi, ya lashe kambun Hukumar Kwallon Kafa ta duniya (FIFA) na “Gwarzon Dan Wasa” a 2023.

A ranar Litinin FIFA ta mika dan wasan wanda dan asalin Argentina ne kambun a birnin bayan da ya doke dan wasan Manchester City, Erling Haaland.

Haaland ya samu damar lashe kambun bayan da ya zira kwallo sau 52 a raga a matsayin dan wasan Manchester City.

Amma Messi ya lashe zaben ne bayan ya lashe gasar Ligue 1 a Paris Saint-Germain da kuma gasar Leagues Cup ‘yan wstanni bayan da ya koma Inter Miami.