Fabrairu INEC za ta sake zaɓen wasu mazaɓu da na cike-gurbi – Shugaban INEC

Daga BASHIR ISAH

Ya zuwa watan Fabrairu na baɗi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke sa ran sake zaɓuɓɓuka a wuraren da akwai buƙatar haka a sassan ƙasa.

Shugaban hukumar na ƙasa, Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron da suka yi da jam’iyyum siyasa a ranar Litinin.

“Game da zaɓen cike gurbi, idan ba a manta ba a jawabin da na yi a lokacin rantsar da Kwamishinonin Zaɓe (RECs) haɗe da taron zangon ƙarshe da muka yi da baƙi ɗaya kwamishinonin zaɓe na ƙasa, na ce hukumar za ta gudanar da zaɓe domin cike guraben da ke akwai a majalisar tarayya da na jihohi,” in ji Mahmoud.

Ya ƙara da cewa, “Hukumar na hanƙoron gudanar da zaɓuɓɓukan a makon farko na watan Fabrairun 2024, wato dai kimanin wata guda da ‘yan kwanaki ke nan kafin sake sabon zaɓe da na cike gurbi.”

Sai dai ya ce kafin ayyana ranar da za a gudanar da zaɓuɓɓukan, INEC za ta kira taro don cimma matsaya.

“Bayan taron tuntuɓa, hukumar za ta yi taro domin nazari kan shirye-shirye sannan ta tsayar da rana, wannan ya ƙunshi har da jadawali da kuma bayanin lokutan yadda ayyukan zaɓuɓɓukan za su gudana,” in ji shi.