Ambasadar EU ta ziyarci jihar Nasarawa a karon farko

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Ambasadar Ƙasashen Yamma, wato European Union a Nijeriya, Samuela Isopi ta bayyana niyar ƙasashen yamman na haɗa kai da gwamnatin jihar Nasarawa a fannin bunƙasa tattalin arziki na zamani da noma da sauyin yanayi don cigaban jihar baki ɗaya.

Ambasada Isopi ta bayyana haka ne a jawabin ta a lokacin da ta kai ziyarar aiki jihar Nasarawa inda ta gana da Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule a gidan gwamnati da ke Lafiya a cikin mako da ake ciki.

Acewarta maƙasudin ziyarar ta shi ne don ƙarfafa dangantaka tsakanin EU da jihar Nasarawa da kuma fara gudanar da wasu ayyukan cigaba da dama a jihar da suka haɗa da inganta fannin tsaron jihar da tattalin arziki irin na zamani da sauyin yanayi da mulki da dai sauran su.

Isopi wadda ita ce ambasadar EU a Ƙungiyar ECOWAS, ta bayyana cewa abinda kawai EU ɗin ke buƙata shi ne aiki tare da gwamnatin jihar Nasarawar wajen kawar da ƙalubalan dake tsakanin duka ɓangarorin biyu.

Ta ci gaba da cewa, “Ba shakka kawo yanzu EU ta gano akwai matsaloli da dama dake ci gaba da addabar jihar Nasarawa da suka hafa da canjin yanayi da tsarin mulki da tsaro da ilimi da kuma kiwon lafiya da sauran su.

“Shi ya sa muka ga ya dace muzu mu haɗa hannu da ku mu kuma tallafa muku don tabbatar mun shawo kan matsalolin tare”, inji ta.

A nasa ɓangaren da yake mai da martanin jawabi gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya bayyana godiyarsa ga Ambasadar dangane da ziyarar wadda ya bayyana a matsayin mai ɗimbin tarihi kasancewar wannan shi ne karon farko da Ambasadar ta ziyarci jihar inda ya jaddada cewa, jihar Nasarawa da Nijeriya baki ɗaya za su ci gaba da aiki tare da EU akoyaushe idan aka yi la’akari da ayyukan agaji da tallafi wa al’umma baki ɗaya da EU ɗin ke ci gaba da gudanar a faɗin ƙasar nan baki ɗaya kawo yanzu.

Ya ce a shirye gwamnatin sa take ta hada hannu da Ambasadar wajen cimma duka burin da ta ayyana a jawabin ta da suka shafi cigaban jihar a duka matakai.

Gwamna Sule ya ƙara da cewa duk da cewa kawo yanzu gwamnatinsa tana ci gaba da aiwatar da wasu kyawawan shirye-shirye dake cigaba da daƙile wadannan ƙalubalai amma duk da hakan idan EU din za su agaza wa gwamnatin sa a waɗannan fannonin ba shakka a kan zai samar da nasarori da dama a jihar a kowane fanni.