Daga UMAR GARBA a Katsina
Ɓarayin daji sun saki sauran ɗaliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutsinma a jihar Katsina, wato FUDMA, bayan shafe fiye da wata biyu a hannun ɓarayin.
Shugaban makarantar, Farfesa Arma Ya’u Hamisu Bichi ne ya shaida wa BBC cewa ya samu labarin sakin ɗaliban daga ɗaya daga cikin mahaifan ɗaliban a yammacin ranar Asabar.
Tun farko Blueprint Manhaja ta bayyana cewar, a ranar 4 ga watan Oktoba, wasu ‘yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kutsa kai a wani gida kusa da makarantar Mariamo Ajiri a ƙaramar hukumar Dutsinma inda ɗaliban ke haya suka kuma yi awon gaba da su.
Kazalika, a ranar 22 ga watan Nuwamba, 2023 MANHAJA ta bayyana cewa ɗaya daga cikin ɗaliban mata biyar da ɓarayin dajin ke garkuwa da su don neman kuɗin fansa ta kuɓuta daga hannunsu bayan shafe kwanaki hamsin a tsare.
Yanzu dai a iya cewa dukkan ɗaliban sun koma gidajensu kamar yadda shugaban jami’ar ya bayyana.
Farfesa Bichi ya kuma ce, a iya saninsa ba a biya diyya ba don sakin ɗaliban.
A ƙarshe, ya gode wa mai ba wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu da kwamishinan ‘yan sandan jihar da kuma daraktan hukumar tsaro ta DSS bisa ƙoƙarin da da ya ce sun yi wajen sakin dukkan ɗaliban biyar.
