Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mista Sidie Tunis, Shugaban Majalisar ECOWAS, ya ce za a ɗage takunkumin da aka ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar, idan har gwamnatin soja ta saki Shugaba Mohamed Bazoum.
Shugaban majalisar ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da tawagar mutane 19 daga ƙungiyar ‘yan Afrika suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja.
Ziyarar dai ita ce ta sanya majalisar ta goyi bayan ɗage takunkumin da aka ƙaƙaba wa Nijar domin rage raɗaɗin da talakawa ke fuskanta a ƙasar.
Shugaban majalisar ya buƙaci tawagar da ta saki Bazoum da iyalansa ba tare da wani sharaɗi ba, tare da sanya wani ɗan gajeren lokaci don mayar da ƙasar bisa tsarin mulkin dimukraɗiyya.
A cewar Tunis, ba tare da la’akari da yunƙurin da ƙungiyar ta yi ba, ba a sami wani sakamako mai kyau ba tun bayan da gwamnatin mulkin soja ta kawar da zaɓen dimokuraɗiyya a Nijar.
“Mun fi sha’awar abubuwan da ke faruwa a Nijar, mun aika da tawaga domin su binciki halin da ake ciki bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, amma muna buƙatar ku a matsayinku na ‘yan ƙasa da ku taimaka wajen rage tasirin.
“Muna wakiltarku a matsayin ‘yan majalisar ECOWAS; Diflomasiyyar ‘yan ƙasa a ra’ayina ita ce mafi kyawun tsarin diflomasiyya wanda idan aka yi amfani da shi da kyau zai iya magance matsalolin da yawa, ba kawai a wannan yanki ba har ma a duk nahiyar Afirka.”
