Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan magatakardan Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen gwamnan Jihar Kogi, David Umar Mike, tare da kwashe takardun masu ƙara.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar (PPRO), SP William Aya, ya bayyana hakan a Lokoja ranar Laraba.
Hukumomin ‘yan sandan sun ce maharan da suka kai harin na sakatariyar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar sun kwashe dukkanin takardun ƙarar da wasu jam’iyyun siyasa biyar suka shigar.
A cewar hukumomin ’yan sanda, takardun da aka kwace daga hannun Mike sun haɗa da, ƙorafe-ƙorafen da jam’iyyu huɗu (4): Action Alliance (AA), Action People’s Party (APP), Peoples Redemption Party (PRP) da Social Democratic Party (SDP) suka shigar, haka kuma Littattafai guda biyu (2) na ƙara da ke ɗauke da bayanan sirri.
Rundunar ’yan sandan ta ƙara da cewa, lamarin ya faru ne daf da ofishin babban bankin Nijeriya (CBN) da misalin qarfe 1320 na ranar Litinin, yayin da waɗanda lamarin ya rutsa da su ke kan hanyarsu ta zuwa harabar kotun da ke babbar kotun jihar, Lokoja.
’Yan sandan sun ce, “A ranar Litinin, 04/12/2023 da misalin ƙarfe 1820, wani David Umar Mike sakataren kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi tare da Labode Apreala sakataren sirri da Hassimu Adamu mataimakiyar sakatare, suka zo jihar. Sashen binciken manyan laifuka, hedikwatar ’yan sandan Jihar Kogi, ta ruwaito cewa, a ranar da aka ce, uku daga cikinsu sun bar ɗakunansu na otel da ke Lokoja da misalin ƙarfe 1300 na safe, inda suka nufi ofishinsu da ke harabar babbar kotu a cikin motarsa (Peugeot 406).
SP Aya ya ƙara da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Onuoha Benthrand, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan ta shawarci jama’a da su guji kalaman da za su iya ɓata damar gudanar da bincike a kan lamarin duk da cewa rundunar ta yi kira ga duk wanda ke da bayanai kan lamarin da ya bayar da su.
Jam’iyyun SDP da APC sun yi musayar kalamai kan harin da aka kai ranar Litinin inda ɓangarorin biyu ke nuna wa juna yatsa na zargin juna.
Yayin da SDP ta yi zargin cewa wasu ’yan bangar siyasa ne suka kai harin, APC ta ce an kai harin.
