An yanke hukuncin kisa ga sojan da ya kashe Sheikh Goni Aisami

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga sojan da ya kashe fitaccen malamin Musulunci a Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.

Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zama a garin Potiskum, ta yanke wa korarren sojan, Las Kofur John Gabriel hukuncin rataya ne a ranar Talata.

Alƙalin kotun, Usman Zanna Mohammed, ya kuma yanke wa abokin lafinsa, Las Kofur Adamu Gideon, hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan yari.

Mai shari’a Usman Zanna Mohammed ya yanke wa Gabriel hukuncin ne ƙarƙashin dokar soja.

Sojan da za a rataye yana aiki ne da bataliya ta 241 Recce da ke Nguru.
Shi kuma Gideon da ake yanke wa ɗaurin shekaru 10 an same shi ne da laifukan haɗin baki.

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Mohammed ya ce bayan yin nazari sosai kan hujjojin da ke gaban kotun da kuma yadda waɗanda ake tuhumar suka kasa bayar da wasu muhimman shaidu da za su tabbatar da da’awarsu, ya yanke wa waɗanda ake tuhuma hukuncin da ya dace da su.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun kashe  Sheikh Goni Aisami ne a Qaramar Hukumar Karasuwa ta jihar Yobe, a ƙoƙarinsu na ƙwace motar malamin, a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Gashua daga Kano a ranar 22 ga watan Agustan 2022.

Sakamakon haka, gwamnatin jihar Yobe ta hannun ma’aikatar shari’a ta kai ƙara kotu wanda ya kai ga yanke hukunci a ranar wannan Talata 5 ga Disamba, 2023.

By Editor