*Sojoji da al’ummar Nijar ne matsalar ƙasar
Daga BASHIR ALYU
A tsakanin ‘yan makonnin da suka gabata an yi ta yaɗa farfaganda a soshiyal midiya a Jamhuriyar Nijar inda ake zargin Ministan Harkokin Wajen Nijeriya kuma Shugaban Kwamitin Nazari da Tatutuwa Sha’anin Tsaro na ECOWAS, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, na aiki da ra’ayin ƙasashen yamma musamman Faransa, wajen neman kuɓutar da Shugaba Bazoum da kuma ayyana lokacin da sojojin juyin mulki za su miƙa ragamar mulkin ƙasar.
Juyin mulkin da ya auku a Nijar abu ne da ba za a lamunci aukuwarsa ba a ko’ina, kuma Nijeriya na da nauyin kare dimokuraɗiyyar da ya rataya a wuyanta ƙarƙashin hulɗarta na harkokin waje, kuma takunkumin tattalin arzikin da aka ƙaƙaba wa Nijar wanda ya ƙuntata wa rayuwar al’ummar ƙasar ba da nufin muzguna wa ‘yan ƙasar aka yi hakan ba sai don matsa wa sojojin juyin mulki lamba don su amince da zaman sulhu wanda hakan ka iya zama silar sakin Shuhgaba Bazoum sannan ƙasar ta sake komawa kan turbar dimokuraɗiyya kamar yadda aka san ta a baya.
Ƙaƙaba wa Nijar takunkumi da Nijeriya ta jagoranta hakan ya faru ne tare da kulawar mambobin ECOWAS, sannan Nijeriya na da munufofinta da ta keɓanta da su wanda ba shi yiwuwa wata ƙasa ta yi amfani da su. Don haka babu wani amfani zargin Ministan Harkokin Wajen Nijeriya da yin munafurci.
A martanin da ya yi kan batun cewar Nijeriya ta bada himma wajen shiga da fita kan batun Nijar a madadin Faransa ko wata ƙasa mai mai faɗa a aji, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya yi watsi da shaci-faɗin da ake yaɗawa, tare da cewa Nijeriya na da daɗaɗɗen tarihi wajen bai wa dimokraɗiyyar Afirka kariya.
“Kowa ya san kyakkyawan tarihin Nijeriya idan ana batun tsayin daka wajen yin abin da ya kamata, ta yi rawar gani a gwagwarmayar samun ‘yancin walwala a ƙasashen Afirka ta Kudu, Zimbabwe, Angola da Mozambique.
“A kowane lokacin muna nan don bada gudummawa, kuma mun tabbata a kan haka. Muna ganin abin da muke yi game da Falasɗin da kuma abin da ke faruwa a Gaza. Wannan shi ne kwatankwacin abin da muke cewa game da halin da Nijar ke ciki.”
An rawaito Ambasada ya yi waɗannan kalaman ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron COP28 da ya gudana kwanan nan a Dubai.
Ashe ba mu lura cewa an samu aukuwar juyin mulki har sau shida a yankin Afirka ta Yamma a tsakanin shekara biyu ba, lamarin da ya shafi ƙasashen Burkina Faso, Mali, Guinnea Bissau da Nijar wanda baki ɗayan ƙasashen mambobin ECOWAS ne, hakan kuwa babban koma baya ne ba ga fannin dimokraɗiyya da dokar da ta kafa ECOWAS kawai ba, har ma da fannonin tsaro da ayyukan jinƙai a yankin.
Tun bayan da aka kauce wa hatsarin amfani da ƙarfin soji wajen maido da tsarin dimokuraɗiyya a Nijar, ragamar harkokin Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta koma hannun Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, kuma ya ci gaba da gudanar da harkokin ma’aikatar daidai da ƙudirin Shugaba Tinubu Doctrine. Don haka, ana buƙatar ɗaukar matakan da suka dace don dakatar da yanayin da kuma daƙile masu haifar wa sha’anin mulki cikas.
Akwai kiraye-kirayen neman ECOWAS ta ɗage takunkuman da ta ƙaƙaba wa Nijar, sai dai manufar ɗaukar wannan mataki shi ne domin maido da daidaito a Nijar da Mali da Burkina Faso wanda suke fuskantar ƙaruwar hare-haren ta’addanci.
A cewar Omar Alieu, Shugaban ECOWAS, sha’anin tsaro na daɗa taɓarɓarewa a Mali da Burkina Faso da Nijar inda sama da mutum miliyan 4.8 ke neman agaji sakamakon hare-haren ta’addanci, sannan sama da mutum miliyan biyu sun rasa matsugunnansu.
Babu mai musun cewa takunkuman da aka sanya wa Nijar ba su ƙuntata wa takakawan ƙasar, sai dai Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da Shugaban ECOWAS sun bayyana cewa har yanzu ƙofa a buɗe take domin tattaunawa da sojojin juyin mulkin ƙasar.
A saki Bazoum domin ya tafi wata ƙasa ta daban, sannan idan sojojin juyin mulkin suka taɓuka wajen samar da cigaban da za ta bada damar dawo da mulkin farar hula sannan ne za a ɗage tankunkuman, kana hulɗar Nijar da maƙwabtanta ta koma yadda aka san ta a baya.
Ya kamata sojojin juyin mulki da al’ummar Nijar su fahimci cewa ba Tuggar ne matsalar ba, amma su ne matsalar kansu. Gara dai tun wuri su miƙe su yi abin da ya kamata tun kafin lokaci ya ƙure musu.
Bashir Aliyu, mai sharhi ne kan shiyyoyin siyasa, kuma ya rubuto ne daga Abuja.
