Gwamnatin Zamfara ta ƙwato motoci 50 daga hannun Matawalle

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce, ta kwato motoci kusan 50 mallakin gwamnatin jiha da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya tafi da su.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Gusau, Sani Sambo, mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Sokoto ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya qara da cewa, an bi tsarin da ya dace domin kwato motocin daga gidajen Gusau da Maradun na tsohon gwamnan wanda a baya ya musanta cewa ya mallaki kadarori ne tun kafin ya zama gwamna.

Sambo ya bayyana cewa, gwamnatin da Gwamna Dauda Lawal ke jagoranta tana yin duk mai yiwuwa domin ganin an kawo cigaban da ake so a jihar amma ba wai don farautar kowa ba ko kuma yi wa wani tozarci ba.

Cikin gaggawa tsohon gwamnan ya tabbatar da hukuncin kotu da ya hana gwamnatin jihar yin irin wannan aiki, har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukunci kan lamarin.

A cewar gwamnatin jihar, kotu a Sokoto ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan ya kai mata.