Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya 9,000 daga 13,000 sun faɗi jarrabawar ƙarin girma

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Aƙalla ma’aikatan gwamnati 9,000 da suka zana jarrabawar ƙarin girman ma’aikatan Gwamnatin Tarayya na shekarar 2022 sun faɗi.

An samu wannan adadi ne daga Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta Tarayya.
An ce aƙalla ma’aikatan gwamnati 13,000 ne suka zana jarrabawar ta shekarar 2022, wadda aka gudanar a kusan cibiyoyin gwajin kwamfuta 69.

An zaɓo ma’aikatan ne daga manyan ma’aikatan gwamnati, ’yan sandan Nijeriya, da sauran jami’an soji da sauran hukumomin tsaro.

Wasiƙar mai ɗauke da jerin sunayen ma’aikatan da suka yi nasara ta kasance a ranar 30 ga Nuwamba, 2023 kuma an aiko ta daga Hukumar Kula da Ma’aikata ta Tarayya.

Wasiƙar mai suna FC.6241/S.35/Vol.xi/T12/268, ta samu sa hannun daraktan ƙara wa juna sani Bello, kuma ta aikewa ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya.

A cikin jerin adadin da aka maƙala a wasiƙar, an lura cewa ma’aikatan gwamnati 3,851 ne kawai suka samu nasara daga cikin sama da ma’aikatan gwamnati 13,000 da suka zana jarrabawar ƙarin girman.

A cikin adadin, an bayyana cewa, alal misali, jami’ai 139 ne aka ƙara musu girma daga muƙamin mataimakin babban jami’in gudanarwa zuwa babban jami’in gudanarwa.

A cikin wata wasiƙar yabo ta Babban Sakatare, Ofishin Gudanar da Ma’aikata na OHCSF, Marcus Ogunbiyi, an sanar da ma’aikatan gwamnati cewa karin girma ga ma’aikatan gwamnati na shekarar 2023 a ofishin shugaban ma’aikatan Gwamnatin Tarayya zai gudana daga Disamba 11, 2023 zuwa Disamba 16, 2023.