Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun afka wa al’ummar Gandu tare da yin garkuwa da wasu ɗalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia.
Wani ɗalibin jami’ar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun zo ne da farko a yawansu da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Laraba inda suka fara harbi a iska don tsoratar da mazauna yankin, amma daga baya sun fara harbi kan mai uwa da wabi, lura da cewa jami’an tsaro na tahowa sai suka tsere cikin daji domin su ɓuya na tsawon sa’o’i.
Wani ganau, wanda kuma bai so a buga sunansa ba, ya shaida cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki wani otel na taro da ke kan titin Makurdi kusa da rukunin gidajen Nasarawa a ranar Alhamis da ƙarfe 2 na safe, suka yi garkuwa da ɗalibai biyar.
A cewar majiyar, ’yan bindigar sun sake tayar da zaune tsaye a garin Gandu da ke kusa da jami’ar, inda suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya tilasta wa ɗaliban ficewa daga gidansu.
Rahotanni sun ce sun yi awon gaba da ɗalibai biyar ne a yayin da suke hakan, yayin da da dama suka jikkata.
An tattaro cewa, ‘yan bindigar sun shafe kusan sa’o’i uku suna gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim ya bayyana cewa kawo yanzu ba a tantance adadin ɗaliban da aka sace ba, amma ya ce ɗalibai uku ne zuwa biyar.
Ya ce, “Ya yi wuri a iya tantance adadin ɗaliban domin waxanda abin ya shafa ba a cikin harabar makarantar suke zaune ba, a wajen harabar makarantar ne.
“Daga bayanan da ake samu, adadin ɗaliban da aka sace ya kai tsakanin uku zuwa biyar. Kodayake, jami’ar tana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa duk ɗalibai suna zaune a cikin harabar makarantar.”
A halin da ake ciki, ɗaliban jami’ar sun gudanar da zanga-zangar lumana, inda suke neman a kawo qarshen satar ɗaliban da ake cigaba da yi.
An ruwaito cewa, sace ɗalibai ya zama ruwan dare gama gari a cikin jami’ar domin a halin yanzu ɗaliban na rayuwa ne cikin fargaba.
An yi garkuwa da ɗalibai sama da 15 na jami’ar a wannan zangon karatu tare da biyan maƙudan kuɗin fansa a cikin taɓarɓarewar tattalin arzikin ake ciki.
Ɗaya daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a baya, wanda ya zanta da manema labarai a Lafiya ya ce, “Mu biyar ne, ciki har da wata mace. ’Yan bindigar sun yi ta dukanmu da yi mana barazana kuma suka cigaba da tafiya muna gudu har tsawon dare.
“Daga baya sun karɓi Naira 500,000 daga hannun iyayena suka sake ni. Ban san abin da ya faru da sauran ba saboda ba za su iya biya ba.”
