Siyasa

Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP

Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya ta ce hana ta ƙwace mata zaven da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka. Wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami'i mai binciken kuɗi na jam'iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Ƙasashen Yamma ranar Laraba, NNPP ta yi iƙirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunƙurin yi wa zaɓen mafi rinjayen al'ummar Kano zagon ƙasa. 'Ya'yan jam'iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: An naɗa sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: An naɗa sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa

Daga BASHIR ISAH 'Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun zaɓi Danladi Jatau a matsayin sabon Kakakin da zai ci gaba da jagorancin majalisar. A ranar Juma'a aka naɗa Jatau a matsayin sabon shugaban majalisar jihar biyo bayan tsige Ibrahim Balarabe Abdullahi da Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta yi daga kujerasa. Kazalika, 'yan majalisar sun naɗa Mohammed Oyanki a matsayin Mataimakin Kakakin majalisar. Jatau na wakiltar shiyyar Kokona ne a majalisar, yayin da Oyanki ke wakiltar mazaɓar Doma ta Arewa.
Read More
2024: Babu abin da zai dakatar da ni daga takarar Gwamnan Edo – Shaibu

2024: Babu abin da zai dakatar da ni daga takarar Gwamnan Edo – Shaibu

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Gwnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya bayyana aniyarsa ta neman shiga takarar gwamnan jihar ya zuwa 2024. Ya ce zai tsaya takarar ne a ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, tare da cewa, babu abin da zai hana shi neman kujerar gwamnan jihar. Shaibu ya bayyana aniyyar tasa ce da safiyar ranar Litinin a cibiyar Biohop Kelly Centre da ke Benin City, babban jihar. Da yake yi wa dandazon masoyansa jawabi, Shaibu ya ce a matsayinsa na ɗan asalin jihar wanda kuma ya san ciwon al'ummar jihar, zai nemi shugabancin jihar ne don cigabanta da ma al'ummarta baki ɗaya.…
Read More
Shari’ar kotunan Nijeriya ta zama tufka da warwara – PDP

Shari’ar kotunan Nijeriya ta zama tufka da warwara – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Nijeriya, ta bayyana hukunce-hukuncen da kotunan ɗaukaka qara suka yi, inda suka ƙwace nasarar wasu gwamnoni a matsayin "karan-tsaye" ga dimokraɗiyya. Jam'iyyar adawar na zargin APC mai mulkin Nijeriya ne da "amfani da qarfin iko" wajen tanqwara hukuncin kotunan, zargin da APC ta musanta. "Shari'ar Nijeriya ta zama kamar rawar 'yan mata yanzu; idan an yi gaba, sai a koma baya," inji Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi. Ya ce dalilan da mutanen nan ke gabatarwa suna kwace zaɓen nan, akasari batutuwan da suka shafi kafin zaɓe…
Read More
Muna maraba da kafa jam’iyyar haɗaka kamar yadda Atiku ya nema – NNPP

Muna maraba da kafa jam’iyyar haɗaka kamar yadda Atiku ya nema – NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya ta nuna aniyarta ta shiga jam'iyyar haɗaka da sauran jam'iyyun adawa kamar yadda Atiku Abubakar ya nema a makon da ya gabata. Ɗan takarar na jam'iyyar PDP a zaven shugaban Nijeriya na 2023, Atiku ya zargi APC da yunƙurin mayar da Nijeriya bin tsarin jam'iyya ɗaya sannan ya yi kira ga jam'iyyun adawa da su dunqule don yin waje da jam'iyyar mai mulki. Shugaban Riƙo na NNPP na Ƙasa, Abba Kawu Ali, ya faɗa a yau Talata yayin wani taron manema labarai cewa kiran na Atiku abin a…
Read More
APC zaɓe ko ƙwace?

APC zaɓe ko ƙwace?

Ga dukkan alamu jam'iyya mai mulki APC tana daf da kwace duk kujerun gwamnonin arewa. Jihar Kano ce ta farko wajen yiwuwar ta zamo ta APC amma idan Kotun Ƙoli ta tabbatar da hakan. Sai jihar zamfara wacce ga alamu sai an sake zaɓe a wasu yankuna a tsakani gwamnan PDP mai karagar mulki da kuma tsohon gwamna na APC wanda minista ne a yanzu. Jihar Filato ma a cen kotu ta kwace kujera ta gwamnan PDP ta mayar ga gwamnan APC wanda su kai takara. Amma mu kula da kyau? Dukkanin inda a ke ƙwace kujeru na gwamnoni ko…
Read More
Kotu ta bada umarnin sake zaɓe a mazaɓar Kakakin Majalisar Bauchi

Kotu ta bada umarnin sake zaɓe a mazaɓar Kakakin Majalisar Bauchi

Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta bada umarnin kan a sake gudanar da zaɓen Ningi ta Tsakiya a Ƙaramar Hukumar Ningi, Jihar Bauchi. Kakakin Majalisar Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, shi ne mai wakiltar Ningi ta Tsakiya a majalisar. A zaman da ta yi a ranar Juma'a, Kotun ta bada umarnin a sake zaɓe a rumfunar zaɓe guda 10 a yankin. Baturen zaɓe daga INEC, Farfesa Shuaibu Muhammad ne ya bayyana Suleiman a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, 2023. Suleiman wanda ɗan Jam'iyyar PDP ne, ya lashe zaɓe a…
Read More
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule

Daga BASHIR ISAH A ranar Alhamis Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Nasarawa inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar. A watan Oktoban da ya gabata ne Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a jihar ta soke nasarar Gwamna biyo bayan ƙarar da Jam'iyyar PDP a jihar da ɗan takarar Ombugadu suka shigar suna ƙalubalabtar sakamakon zaɓen. Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce ƙaramar kotun ƙarƙashin jagorancin Ezekiel Ajayi, ta tafka kuskure a hukuncin da ta yanke musamman wajen yin amfanin da bayanan shaidu ba bisa…
Read More
Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara: Gwamna Abba ya garzaya Kotun Ƙoli

Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara: Gwamna Abba ya garzaya Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya garzaya Kotun Ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na soke nasarar da ya samu a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Kano. Wannan wata alama ce mai nuni da Gwamna Abba ba zai bari ya yi ƙasa a gwiwa bs wajen kare kujerarsa a matsayin Gwamnan Kano. Haka nan, wannan shi ne matakin kotu na ƙarshe da Yusuf zai ɗauka don kare kujerar tasa. Kwannan ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe, inda ta sauke Gwamna Abba na Jam'iyyar NNPP daga kujerar gwamnan Kano tare da…
Read More
Kowa ya zarce a zaɓen gwamnan Bayelsa, Imo da Kogi

Kowa ya zarce a zaɓen gwamnan Bayelsa, Imo da Kogi

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa zaɓen da ya gudana a ƙarshen mako ya zama zarcewa da kowace jam'iyya da ke kan gado a jihohin. Gabanin shiga zaɓen, mun yi bayani a makon jiya na yadda a ka fara har jihohi 7 su ka zama waje da sauran jihohi a lokacin gudanar da babban zave. Sakamakon shari'un kotu su ka sauya lokutan zaɓen jihohin. Yanzu ma ba abun mamaki ba ne waɗanda ba su gamsu da sakamakon zaɓen ba su sake garzayawa kotu don neman a yi sabon lale. Nan gaba ma akwai zaɓen gwamnan jihar Edo da Ondo. Abun…
Read More