Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara: Gwamna Abba ya garzaya Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya garzaya Kotun Ƙoli domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na soke nasarar da ya samu a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Kano.

Wannan wata alama ce mai nuni da Gwamna Abba ba zai bari ya yi ƙasa a gwiwa bs wajen kare kujerarsa a matsayin Gwamnan Kano.

Haka nan, wannan shi ne matakin kotu na ƙarshe da Yusuf zai ɗauka don kare kujerar tasa.

Kwannan ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe, inda ta sauke Gwamna Abba na Jam’iyyar NNPP daga kujerar gwamnan Kano tare da ayyana Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano.