Katsina: Raɗɗa ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da shirin rigakafin dabbobi na shekarar 2026 domin daƙile da kuma shawo kan manyan cututtuka masu yaɗuwa da ke addabar shanu, tumaki da awaki a faɗin jihar.

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a kauyen Fulanin Shifdawa da ke Karamar Hukumar Batagarawa, inda aka fara aikin rigakafin a dukkan sassan jihar domin yaki da cututtukan Contagious Bovine Pleuropneumonia (CBPP), Foot and Mouth Disease (FMD) da kuma Peste-des-Petits Ruminants (PPR).

A jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan shiri wani muhimmin mataki ne na kare lafiyar dabbobi, kara yawan amfaninsu da kuma kare lafiyar al’umma, yana mai jaddada cewa kiwon dabbobi na daga cikin ginshikan tattalin arzikin jihar.

Ya ce rigakafi na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen hana barkewar cututtuka masu yaduwa a tsakanin dabbobi.

“Jihar Katsina ta kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana domin yaki da cututtukan CBPP, FMD da PPR. Rigakafi na da matukar muhimmanci wajen hana barkewar cututtuka da tabbatar da samun lafiyayyun dabbobi masu amfani,”Inji Dikko.

Ya ce tarihin jihar Katsina a harkar kiwon dabbobi da cinikinsu, wata tsohuwar al’ada ce da aka gada tun kaka da kakanni.

“Jihar Katsina na da dadadden tarihi a harkar kiwon dabbobi, kuma sanannen fata na Morocco Leather da ake kasuwancinsa a Arewacin Afirka da Turai, ya samo asali ne daga wannan yanki,” in ji shi.

Ya kara da cewa duk da muhimmancin da bangaren kiwon dabbobi yake da shi ga rayuwar al’umma, har yanzu yana fuskantar manyan kalubale sakamakon barkewar cututtuka da ke rage yawan amfaninsu tare da barazana ga wadatar abinci.

“Cututtukan nan guda uku—CBPP, FMD da PPR—na daga cikin manyan matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban kiwon dabbobi, suna haddasa mace-macen dabbobi, rage yawan amfaninsu tare da jawo asarar tattalin arziki mai yawa,” ya bayyana.

A cewarsa, aikin rigakafin zai gudana a dukkan mazabu 361 da ke cikin kananan hukumomi 34 na jihar, kuma zai dauki kwanaki 18.

Ya bayyana cewa za a kwashe kwanaki 12 ana gudanar da rigakafin PPR daga gida zuwa gida, yayin da za a yi kwanaki 6 ana gudanar da rigakafin cututtukan CBPP da FMD a fadin jihar baki daya.

Gwamna Radda ya kuma yi nuni da muhimmancin Katsina a matsayin cibiyar kiwon dabbobi sakamakon iyakarta da Jamhuriyar Nijar da kuma yawan zirga-zirgar dabbobi ta hanyoyin kiwo da kasuwanci tsakanin kasashe.

“Kasancewar Katsina jiha ce mai iyaka, tana karbar dumbin dabbobi daga kasashe da jihohi makwabta, wanda hakan ya sanya wannan shiri ya zama mai matukar muhimmanci wajen dakile cututtuka da kuma kare lafiyar al’umma,” in ji shi.

Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na kara inganta ayyukan likitocin dabbobi, bunkasa harkar kiwo da kuma tsarin noma bisa ka’idojin kasa da kasa.

Ya yabawa masu ruwa da tsaki da abokan hulda na ci gaba da suka hada da ƙungiyoyin IOM, UNDP da Co-group bisa irin gudunmawar da suke bayarwa ga bangaren.

Gwamna Radda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa lafiyar dabbobi, wadatar abinci da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar muhimmanci.

“Ina nan daram wajen karfafa tsarin kula da lafiyar dabbobi da kuma bunkasa tattalin arziki mai dorewa a fadin jihar,” ya kara da cewa.

Ya kuma yi kira ga masu kiwon dabbobi, makiyaya, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su ba da cikakken hadin kai ga ma’aikatan rigakafin domin tabbatar da nasarar wannan shiri.

Tun da farko, Kwamishinan raya kiwon Dabbobi na Jihar Katsina, Farfesa Ahmed Bakori Mohammed, ya bayyana cewa jihar Katsina ta dade tana da tarihi mai armashi a harkar kiwon dabbobi, yana mai cewa kiwon dabbobi wata hanya ce ta rayuwa ga dubban iyalai a fadin jihar.

Ya sake tunatar da muhimmancin wannan bangare ta fuskar tarihi, inda ya tuna da irin gudunmawar da Katsina ta bayar wajen samarwa da fitar da sanannen fata na Morocco Leather zuwa kasuwannin Arewacin Afirka da Turai.

Kwamishinan ya gargadi cewa cututtukan CBPP, FMD da PPR na ci gaba da barazana ga yawan amfanin dabbobi, wadatar abinci da lafiyar al’umma, yana mai jaddada bukatar ci gaba da gudanar da shirye-shiryen rigakafi cikin hadin gwiwa.

Ya ce rigakafi na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen yaki da cututtuka masu yaduwa da kuma kara yawan amfanin dabbobi.

A cewarsa, wannan shiri ba wai kare dabbobi kawai zai yi ba, har ma zai taimaka wajen kara karfin garkuwar dabbobi, inganta rayuwar al’ummomin karkara da kuma karfafa wadatar abinci a jihar.

Ya bukaci masu kiwon dabbobi da makiyaya su fito su shiga wannan shiri tare da fadakar da sauran jama’a game da muhimmancinsa.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Batagarawa, Yahaya Lawal, ya bayyana kokarin da karamar hukumar ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Haka kuma ya yi kira da a kammala gidajen ‘yan gudun hijira (IDPs) da ake ginawa a Batagarawa tare da gaggauta kammala sauran ayyukan gidaje da ake gudanarwa.

By Babaji

Leave a Reply