
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi martani ga ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC, Peter Obi, akan kiran sa na cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus, inda ta yi watsi da kalaman nasa da kuma bayyana hakan a matsayin yunƙurin ɗauke hankalin jama’a daga muhimman batutuwan ƙasa.
Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga a wata sanarwa ranar Litinin, ya ce Nujeriya ba ta tafiyar da tsarin mulkin majalisa irin na Birtaniya, don haka kwatanta murabus ɗin Firaministan Birtaniya da matsayin Shugaba Tinubu kuskure ne.
Onanuga ya bayyana cewa, gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu cigaba a fannoni daban-daban da suka haɗa da tsaro, tattalin arziƙi, samar da ababen more rayuwa, ilimi da dai sauransu.
Ya ce, an samu ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na gwamnati, bunƙasar kasuwar hannayen jari da kuma ƙaruwar zuba jari daga ƙasashen waje don bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya
Haka kuma, ya zargi Peter Obi da siyasantar da al’amarin a madadin bayar da shawarwari masu amfani, yana mai cewa gwamnatin Tinubu na cigaba da aiwatar da sauye-sauye domin inganta rayuwar al’umma da ciyar da ƙasar gaba.
