Messi ya karya tarihin yawan zura ƙwallo a gasar Kofin Duniya bayan samun na 17

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Zakaran ƙwallon ƙafa na duniya kuma Kyaftin ɗin Argentina, Lionel Messi ya zama ɗan wasa da ya fi zura ƙwallo a raga a gasar Kofin Duniya na FIFA bayan samun damar zura ta 17 da 18 a wasansu da Austria a birnin Dallas.

Messi mai shekaru 39 ya zura ƙwallo na farko ne a raga a minti na 38, lamarin da ya ba shi damar kere tsohon wasan Jamus Miroslav Klose.

Akan haka ne ya karya tarihin da Klose ya kafa na mafi yawan ƙwallaye a gasar da ƙwallaye 16.

Hakan na zuwa ne bayan da Messin ya zura ƙwallo uku a raga a wasan farko da ƙasarsa ta yi da Aljeriya.

A wasan nasu da Austria, Messi ya zubar da bugun fenareti da fari, inda daga bisani ya zura ƙwallo biyu kafin a kammala wasan.

A yanzu dai Argentina ta haye zuwa zagaye da ‘yan 32 duk da cewa sauran wasan ɗaya a wasannin rukunin-rukuni da ake cigaba da fafatawa.

By Babaji

Leave a Reply