Ambaliya: HYPPADEC ta yi murnar dabarun da Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da su

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi

Manajan darakta na hukumar raya al’ummomin da ke zaune yankunan samar da wutar lantarki, ta ƙasa, HYPPADEC, Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa, Katukan Yauri, yayi na’am da aiwatar da dabarun kariya daga afkuwar ambaliyar ruwa da makamantarsu da gwamnatin tarayya ta yi.

Da yake ma ‘yan jarida bayani a garin Zuru, ranar Asabar da ta wuce, Katuka ya ce, wannan tsarin na gwamnatin tarayya ya ƙara ƙwarin-gwiwa ga ƙoƙarin da hukumar HYPPADEC keyi wurin kawo ma al’ummomi ɗauki.

“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnoni 10 da ke yankunan da HYPPADEC ke kula da su, wurin kawo ma jama’a romon dimokuraɗiyya”,

“Kwanan nan ne, majalisar zartaswa ta tarayya, (FEC), ta hannun majalisar ɓunkasa tattalin arziki ta ƙasa, (NEC), ta amince da a fidda makudan kuɗi da nufin magance, musibobin iska da ruwan sama mai ƙarfi da waɗannan al’ummomi ke fuskanta”,

“A yanzu, gwamnatin tarayya ta ɓullo da dabarun hangen-nesa, bata son sai abu ya faru a sa’ilin zata yi shiri, tafi son ta hana afkuwar wata musiba tun kafin ta zo”,

“Wannan ƙarin-ƙarfine ga irin ayyukan da HYPPADEC ke yi wurin hana ambaliyar ruwa da kuma maganceta”,

“Hukumar na gina ma al’ummomi makarantu, tana kuma tona masu rijiyoyin burtsatse, sannan kuma tana samar da kayayyakin sufuri ta ruwa”,

“HYPPADEC na kariya daga salwantar rayuka a tafiye-tafiyen da al’ummomi ke yi cikin jiragen ruwa”,

“HYPPADEC na bai wa jama’a rigunan kariya daga nutsewa a ruwa (life jackets), ko da wata ƙaddara ta gifta”, Katuka ya ce.

By ukarofi

Leave a Reply