PCRC ta yaba da sauye-sauyen IGP tare da jinjinawa Inuwa kan ƙarfafa tsaro a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Kwamitin hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma (PCRC) a Jihar Gombe ya yaba da sauye-sauyen da sufeto janar na ‘yan sanda (IGP) ya ɓullo da su, yana mai bayyana su a matsayin muhimman matakai da za su ƙara ƙarfafa tsarin aikin ‘yan sanda na kusanci da al’umma, inganta amincewar jama’a ga rundunar ‘yan sandan Najeriya, da kuma bunƙasa tsaro a faɗin ƙasar nan.

Shugaban PCRC na Jihar Gombe, Alhaji Garba Muhammad Ubale, ne ya bayyana hakan yayin wani taron hulɗa da al’umma da mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (DIG) mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, Zachariah Fera Achinyan, ya halarta tare da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da wakilan al’umma a Gombe.

Ubale ya ce kwamitin ya gamsu da yadda shugabannin rundunar ‘yan sanda na yanzu ke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin da suke yi wa hidima.

Ya ce, “A madadin kwamitin hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma na Jihar Gombe, muna farin cikin maraba da DIG a jihar. Wannan ziyara ta nuna ƙudirin shugabancin rundunar ‘yan sanda na yin aiki tare da al’umma domin samar da zaman lafiya, tsaro da amincewa tsakanin jama’a da jami’an tsaro.”

A cewarsa, Jihar Gombe na ci gaba da samun gagarumin ci gaba wajen inganta dangantaka tsakanin ‘yan sanda da al’umma sakamakon haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro, masarautun gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya jaddada cewa tsaro alhakin kowa ne, inda ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen daƙile da kuma yaƙi da aikata laifuffuka.

Shugaban PCRC ɗin ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar, yana mai cewa tallafin da gwamnatinsa ke bai wa hukumomin tsaro ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ubale ya taya Gwamna Inuwa Yahaya murnar samun lambar yabo da aka ba shi kwanan nan bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta tsaro da samar da yanayi mai aminci ga mazauna jihar, yana mai cewa wannan karramawa ta nuna irin ƙoƙarinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Haka kuma ya yabawa shugaban PCRC na ƙasa, Alhaji Mogaji Ibrahim Olaniyan, bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma, inganta shugabanci nagari da ƙarfafa tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ya kuma jinjinawa Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Gombe, CP Usman Ahmed Chosu, saboda yadda yake inganta tsarin aikin ‘yan sanda na kusanci da al’umma da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga rundunar ta hanyar tattaunawa da hulɗa da mazauna jihar da sauran masu ruwa da tsaki.

Ubale ya sake tabbatar da aniyar PCRC na ci gaba da mara wa shirye-shirye da manufofin da ke da nufin inganta tsaro, ƙarfafa zaman lafiya da kuma gina kyakkyawar alaƙa tsakanin ‘yan sanda da al’umma baya.

Tun da farko, DIG Zachariah Fera Achinyan ya jaddada muhimmancin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da jama’a, yana mai cewa ba za a iya samun ingantaccen aikin tsaro ba sai da cikakken haɗin kan al’umma.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai masu amfani, yana mai cewa bayanan sirri daga jama’a na daga cikin muhimman hanyoyin da ake amfani da su wajen gudanar da aikin tsaro na zamani.

DIG ɗin ya bayyana cewa ziyararsa zuwa Gombe na daga cikin ƙoƙarin rundunar ‘yan sanda na ƙara kusantar al’umma, tantance dabarun tsaro da ake amfani da su a yankin Arewa maso Gabas, da kuma gano hanyoyin da za su inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.

Masu ruwa da tsakin da suka halarci taron sun sake tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro, tare da kira da a ci gaba da gudanar da irin waɗannan tarurrukan tattaunawa da hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma domin magance sabbin ƙalubalen tsaro da kuma ƙarfafa zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

By ukarofi

Leave a Reply