El-Rufa’i ya shiga tsaka-mai-wuya yayin da kotu ta karɓi hujjojin DSS akan zargin naɗar hirar Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’amura a shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i akan zargin naɗar hirar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu na ƙara girma bayan Babbar Kotun Tarayya ta Abuja a ranar Litinin ta karɓi wasu muhimman hujjoji daga Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) da ke ƙoƙarin tabbatar da zargin akansa.

Wani lauya mai suna Deji Adeyanju, wanda shi ne shaidan masu gabatar da ƙara na biyu ya faɗa wa kotun cewa El-Rufa’i ya taɓa faɗa a wata hira ta gidan talabijin cewa “mun saurari hirar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro.”

Adeyanju ya tabbatar da wannan iƙirari tare da gabatar da hujjoji da suka haɗa da bidiyon hirar da kuma bayaninsa da ya rubuta.

Akan haka ne kotun ta haska hirar da aka yi da El-Rufa’in domin tabbatar da ɗaukar muryar da kuma kalaman da aka yi zargin furta su yayin shirin.

Ana tuhumar El-Rufa’i ne da laifukan da suka shafi zargin sa ido ba bisa ƙa’ida ba a hanyoyin sadarwa, da kuma alaƙa da mutanen da ake zargi da hannu a aikata al’amarin.

Daga bisani alƙalin kotun ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Yuni domin cigaba da gudanar da hukunci a kai.

By Babaji

Leave a Reply