An ɗauke mata da ɗan shugaban jam’iyyar APC a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Bayanai daga ƙaramar hukumar Yauri da ke jihar Kebbi sun bayyana cewa cikin daren Lahadi wayewar garin wannan Litinin waɗansu mutane kan babura sun yi dirar mikiya a gidan shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar mulki ta Yauri Alhaji Abu Manaja inda suka ɗauke matarsa da kuma ɗansa.

Majiyoyin sun bayyana wa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja da cewa da misalin ƙarfe uku na dare ne waɗansu mutane kan babura suka shiga gidan da ke anguwar GRA Yauri suka tafi da mutanen guda biyu sai dai kawo yanzu dai babu wani sahihin bayanin ko su wanene sai dai ana sa ran masu garkuwa da mutane ne domin neman kuɗin fansa.
Yauri dai ta daɗe tana fama da matsalar ɗauki ɗaiɗai daga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa wanda ya sanya yanzu haka magidanta musamman masu abin hannun ba kasafai su ke kwana a gidajen su ba.

Ana hasashen ma ba iyalin sa ne suka zo ɗauka ba amma sai Allah ya sa shi ba ya gida a lokacin.

Kamar yadda majiyar ta ce, babban ƙalubalen mutanen Yauri shi ne, mutanen da ke kai wa waɗannan ɓata-garin bayanai saboda ana tare da su ala kulli halin amma kuma suna yi wa waɗannan mutane aiki.

By ukarofi

Leave a Reply