Sojoji sun halaka ’yan bindiga biyu, sun ceto mutanen da aka sace a Katsina da Sakkwato

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Dakarun Rundunar Atisayen FANSAR YAMMA sun samu gagarumar nasara a hare-haren da suka ƙaddamar akan ’yan ta’adda a jihohin Katsina da Sakkwato, inda suka kashe wasu daga cikinsu tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar, a ranar 21 ga Yuni, 2026, ’yan ta’adda sun yi yunqurin kai hari garin Tureta da ke jihar Sokoto, amma dakarun sun daqile harin tare da korarsu.

Bayan bin sawunsu, sojojin sun ceto mutanen da aka sace tare da kwato shanu da aka sace da kuma babura biyu da ’yan ta’addan ke amfani da su.

Haka kuma, a safiyar ranar 22 ga Yuni, dakarun sun kai samame mavoyar ’yan ta’adda a qaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina, inda suka kashe ’yan ta’adda biyu tare da jikkata wasu da dama.

An kuma qwato bindigar PKT guda xaya, bindigar AK-47 guda xaya da alburusai, babura uku, na’urorin sadarwa, dabbobin da aka sace da sauran kayayyakin da ‘yan bindigar ke amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.

By Babaji

Leave a Reply