An yaba wa Bola Tinubu kan ƙarin albashi da ya yi wa sojoji

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamintin sojoji a Majalisar Dattijai Sanata Abdul’aziz Musa yar’adua ya yaba wa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan ƙarin albashi da yayi wa sojoji daga naira dubu 100 zuwa dubu 180.

A hira da wata kafar sadarwa national update.ng a Abuja, Sanata Abdul’aziz yar’adua ya bayyana wannan ƙarin albashi a matsayin wani jari a harkan tsaron Najeriya.

Sanatan ya ce sabon tsarin albashin da zai fara aiki a wata mai zuwa , “Sojoji 25000 za su amfana da shirin wanda haka ya nuna cikakken goyon baya na gwamnatin Najeriya ga sojojin da ke sadaukar da ruyuwar su wajan kare ƙasa da tabbatar da tsaro,”Inji Sanata Yar’adua.

Shugaban kwamintin sojoji ya bayyana cewa ƙarin kuɗin harkokin yau da kullum daga Naira biliyan 660 zuwa 924 ya nuna ƙudirin gwamnatin na bada kulawa kan jin daɗi da walwalar sojoji don tsaron ƙasa.

“Sojojin Najeriya maza da mata a koda yaushe suna cikin shiri na tunkarar aikace aikacen ta’addanci,garkuwa da mutane da sauran kayan lafiya,domin har ƙarin albashin ya dace duba da yadda suke sadaukar da kai a wajen aiki,” Inji Yar’adua.

Sanatan ya ƙara bayyana cewa ƙarin albashin ya zo daidai lokacin da rundunar sojojin ke samun nasarar yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuka,kan haka suke buƙatar goyon bayan al’ummar Najeriya.

Ya jinjinawa gwamnatin tarayya kan fara aikin faɗaɗa gine ginen rundunonin sojojin da ya ce zai basu ƙarfin gwiwa wajen tunkarar duk wata barazanar tsaro a ƙasar.

Sanata Abdul’aziz Yar’adua ya jaddada ƙudirin kwamintin Sojoji na majalisar na cigaba da gabatar da ƙudirin da za su inganta ruyuwar sojojin,samar da kayan Yaki na zaman da kuɗaɗen tafiyar da hidimar yau da kullun ga rundunar sojojin.

By ukarofi

Leave a Reply