
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta kammala shirin kawo karshen aikin buga fasfuna a ofisoshinta dake jihohin Nijeriya, inda yanzu ta mayar da tsarin bugawa a cibiya guda da ke hedikwatarta Abuja.
NIS ta ɗauki wannan mataki ne da nufin ƙarfafa tsaro, inganta harkar gudanarwa da kuma zamanantar da tsarin samar da fasfo a Nijeriya.
A wata sanarwa da jami’inta na hulɗa da jama’a, Akinsola Akinlabi ya fitar a ranar Laraba, ya ce masu neman samun fasfo za su cigaba da zuwa ofisoshin da suke so, yan ai tabbatar da cewa cibiyoyin za su cigaba da aiki a kai da kuma bayarwa.
A cewar sanarwar, gyaran da aka yi ya ƙunshi samar da wajen wallafawa guda da tsarin tsaro na duk mai son yin fasfo, wanda a ƙarƙashinsa za a riƙa samar da katin fasfo a wani waje mai cike da tsaro a Abuja da kuma rarraba ga ofisoshinsu da ke faɗin Nijeriya cikin makonni biyu kacal.
A cewarta, an zartar da wannan hukunci ne ƙarƙashin tsarin sauye-sauyen da gwamnati take yi a harkokin da suka shafi biza da sauran al’amauran shige da fice, wanda batun kyautata tsarin yin fasfo yake a ciki.
Ana sa ran daga ranar 10 ga Agusta NIS za ta rufe ofisoshin bayar da fasfuna dake jihohin Kano da Kaduna da Birnin Dutse a jihar Jigawa da Gombe da kuma Adamawa, amma ya ce duka wannan tsari bai shafi duk mai bukatar yin fasfo ba a duk inda yake, illa ma dai kara sauka mallakar fasfo din.
