Yadda ake duba jarrabawar kammala sakandare ta 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Shirya Jarrabawar Yammacin Afirka (WAEC), ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare (WASSCE) ta 2026 ga ɗaliban da suka rubuta.

Domin duba sakamakonsu, ana buƙatar ɗalibi ya samo lambobin sirri (PIN) da lambar shaida (serial number) daga sahihin shafin WAEC kafin cigaba da cika ƙa’idojin duba sakamakonsa.

Haka kuma, wajibi ne ɗalibi ya bayar da lambarsa ta jarrabawa, lambar katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da ya yi amfani da ita yayin rajista da wasu bayanansa kafin kammala bin hanyoyin tantancewar.

Ga matakan da ɗalibi zai bi wajen samun duba sakamakon jarrabawarsa ta WAEC kamar yadda jarumar conclave ta wallafa:

“Below is how to get serial number and pin to check 2026 WAEC result:

To get your serial number and pin;

Visit http://waec.org and select the “serial number and pin” menu at the top of the page.

Select the appropriate Examination Year and the Date

Enter your Examination Number and your NIN (Ensure the NIN is the same one that was used during your WAEC registration).

Enter your Email and Phone Number to generate a One-Time-Password (OTP)

Input the OTP to successfully recover your Serial Number and Pin.”

Hakan na zuwa ne bayan hukumar ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar a ranar Laraba, 5 ga Agusta, 2026.

By Babaji

Leave a Reply