Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar sojoji na 17 brigade sun kashe ‘yan bindiga biyu da raunata da dama sun kuma ƙwato makamai a wani samame da suka kai a dajin Ginchawa a ƙaramar hukumar Matazu.
Sojojin sun kai samame bayan da suka sami sahihin bayanin maɓoyar ‘yan bindiga a yankin.
Kaman yadda mai magana da yawun rundunar ta 17 a Katsina,Kaftin Abayomi Adisa ya ce ,sojojin sun Kai mamaya ga ‘yan bindigan a dajin Gachewa inda suka ta ɓarin wuta wanda har ya kai kashe ‘yan bindiga biyu da yawa sun gudu suna ɗauke da raunuka.
Ya ce sojojin sun ƙwato bindaga mai kirar PKT guda biyu da AK47 guda ɗaya da bindida ƙirar gida guda ɗaya da alburusai guda 75.
Sauran kayayyakin da sojojin suka ƙwato akwai baburan hawa guda uku wayan hannu guda biyu, kakin soja da dabbobi.
Kaftin Abayomi ya bayyana cewa babu wanda ya sami ko ƙwarzane daga ɓangaran sojojin.
Rundunar sojojin su sha alwashin cigaba da kai farmaki ga maɓoyar ‘yan bindiga a faɗin jihar har sai sun kakkaɓe su tare da maido da zaman lafiya.
