Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Sule

Daga BASHIR ISAH

A ranar Alhamis Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Nasarawa inda ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

A watan Oktoban da ya gabata ne Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a jihar ta soke nasarar Gwamna biyo bayan ƙarar da Jam’iyyar PDP a jihar da ɗan takarar Ombugadu suka shigar suna ƙalubalabtar sakamakon zaɓen.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce ƙaramar kotun ƙarƙashin jagorancin Ezekiel Ajayi, ta tafka kuskure a hukuncin da ta yanke musamman wajen yin amfanin da bayanan shaidu ba bisa ƙa’ida ba.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uchechukwu Onyemenam, ta ce ba abu ne mai yiwu ba a yi wani ƙorafi da aka shigar kotun sauraren ƙararrakin zaɓe kwaskwarima bayan cikar wa’adin kwana 21 da ayyana kamar dai yadda ƙaramar kotun ta aikata.

Kazalika, Kotun ta yi watsi da batun aringizon ƙuri’un da aka yi zargin an tafka yayin zaɓen.

Alƙali Onyemenam ya ce ƙarar da ɗan takarar Gwamnan PDP ya shigar ba ta da amfani bisa dalilin cewa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ta saɓa ƙa’ida wajen yin watsi da ƙorafin da Gwamna Sule ya shigar.

A ƙarshe dai Kotun ta soke hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke da fari kana ta tabbatar da Gwamna Sule a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Nasarawa.