Isra’ila Ta Jefa Bam Mai Nauyin Ton 2500 A Gaza – Jakadan Falasɗinu

Daga WAKILINMU

Jakadan ƙasar Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh, ya ce mamayar da ƙasar Isra’ila ta yi a Gaza ba komai bane illa ta yi shi da nufin aiwatra da kisan kiyashi. Shawesh ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira a ofishin jakadancin ƙasar na Nijeriya dake Abuja.

Kazalika ya koka kan yadda ake kai hare-haren kan fararen hula babu ƙaƙƙautawa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, da sunan ana yaƙar dakarun Hamas wanda duniya ta san ba haka ba ne. da yake buga misali kan irin rashin imanin da Isra’ila ke yi a Gaza ya bayyana hatta waɗanda ba Falasɗinawa ba, suna jinjinawa gami da tur da al’amarin, inda ya ba da misalin da kalaman Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, kula da Harkokin Jama’a kuma mai kula da Agajin Gaggawa, a cikin hirarsa sa tashar CNN, Martin Griffits, inda ya ce “Ban tava ganin wani abu makamancin wannan irin wannan yanayi a fili ba” a tarihin kisan kiyashi.”

Jakadan ya ci gaba da cewa, a cikin kwanaki 48 na kisan kare dangi a kan al’ummar Palasdinu, abin takaici, kamar yadda ake gani; Ba ni da wani zavi illa na fara da bayani kan adadin da ba shi da daɗin ambato

Sakamakon hare-haren bama-bamai da jiragen yaƙin Isra’ila, da harbin bindiga na na faraɗ ɗaya daga maharbansu, zuwa jerin manyan bindigogi da fasaha na Isra’ila, adadin waɗanda suka mutu a tsakanin Falasɗinawa ya zarce mutum 14,200, cikin waɗannan akwai ƙananan yara kusan 6000, sai kuma mata 4,000, yayin da jimillar adadin ya kai mutum 33,000.

Har ila yau nan kusa mutum Falasɗinawa 6,000 ne suka ɓata a ƙarƙashin ɓaraguzai yayin ake kashe wasu a kan hanya da ake tsintar gawarsu ana yi musu jana’iza cikin mummunan yanayi, kuma duk da wannan hakan ba a damar binne su kamar yadda ya dace ba.

Mutanen da aka kashe a harin da aka kai wa West bank suma adadinsu ya haura mutum 200.

A yankin yammacin Gabar Tekun da suka mamaye, musamman a Ƙauyen Huwara da aka sha fama da hare-hare daga wasu gungun ‘yan ta’adda na Isra’ila, daga cikin wuraren da ake rainon tattalin arziki wanda ke ɗauke da shaguna 300, 45 ne kawai aka ba su damar buɗewa, sauran ana rufe su da umarnin soja. Wannan yana nufin ana tafka babban asarar game da tattalin arzikin Falasɗinu wanda ya samu rauni.

A wani mataki na tabarbarewar tattalin arzikin Falasɗinu, da kuma ƙara cin fuska ga rauni, gwamnatin Isra’ila, waɗanda suke tattara harajimu a madadinmu akan duk wasu samfuran kaya da aka samar, sun karve cikakken iko akan iyakokinmu, sun hana mu duk wata rawar gaban hantsi. Rashin samun waɗannan kuɗaɗe na haraji shi ke haifar da gazawar gwamnatin Plastine wajen biyan albashi da kuma samar da ayyuka.

Kuma bayan dukkan ƙarairayi da furofaganda da suka yi ta yaɗawa kan harin da suka kai asbitin Asshifa da Gaza, daga ƙarshe sun tafka abin kunya, domin abin da suke faɗa na cewa dakarun Hamas na amfani da asibitin wajen aiwatar da ayyukansu an bincika an samu babu wata alamar hakan, sannan kuma har ya zuwa yanzu sun kasa nuna wa duniya shaida guda ɗaya da za ta gaskiyarsu, kuma an kasa samun hakan ko da a cikin kafofinsu kasarsu zamani.

A cikin tattaunawar da ya yi da kafar yaɗa labarai ta CNN, Tsohon Firaministan Isra’ila Euhd Barak, ya yarda da kalamansa da ya yi na “Don masu sadaukarwa muke gudanar da wannan asibiti kuma mun yi hakan ne don mu taimaka musu su gina waɗannan wurare don samun sararin gudanar da asibiti a cikin wannan ɗan karamin wuri”

Muna tabbatar muku da cewa duk wasu muhimman kayan aiki da abubuwan more rayuwa da suka shafi wannan asibiti an lalata shi ta hanyar kai musu hari, babu sauran abubuwan more rayuwa a halin yanzu a Gaza, a halin yanzu ko a yau aka dakatar da wannan hare-hare Gaza ba za tava dawowa wani gari da za a dogara da shi don samun abin more rayuwa ba.

Da aka tambaye shi ko mecece mayarsu kan samar da ƙasshe biyu masu cin gashin kansu? Sai ya ce “Ai su dama tun tuni akan hakan suke, amma ita Isra’ila ita ce ta kafe kai da fata sai dai Falasɗinu su ci gaba da zama a ƙarƙashinsu.”