Hare-haren Isra’ila kan Falasɗinawa: Ban taɓa ganin irin wannan rashin imani ba – Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya, Abu Shawesh ya bayyana cewa, bai tava ganin irin wannan rashin tausayi da tsantsan rashin ba kamar yadda Isra’ila ke ta varin wuta kan fararen hula a Ƙasar Falastɗinu.

Ya ce, Martin Griffiths, a cikin hirarsa ta tashar CNN, ya ce, “bai tava ganin wani abu makamancin haka a baya ba, kisan gilla na rashin imani tsantsa.”

Ya ƙara da cewa, sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama, da harbin bindiga, harbin sari-ka-noƙe, har zuwa saukar da bama-bamai ta sama, adadin waɗanda suka mutu a tsakanin Falasɗinawa ya zarce dubu goma sha huɗu da ɗari biyu (14200), daga cikinsu akwai yara kusan 6000, mata 4000, yayin da adadin waɗanda suka jikkata sun haura dubu 33.

Ya ce, kusan Falastinawa dubu 6 ne har yanzu ake tsammanin suna ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine, yayin da wasu kuma aka kashe a kan tituna ba tare da samun damar tattara gawarwakinsu ba saboda yanayi mai haɗari har ya zuwa yanzu, don haka ba a samu damar binne su cikin sutura na mutuncin da ya kamace su ba.

“Adadin waɗanda suka mutu a yammacin gavar kogin Jordan da aka mamaye ya zarce 200. A yankin yammacin gavar kogin Jordan da aka mamaye, musamman a ƙauyen Huwara – wanda aka sha fama da hare-haren wuce gona da iri da ‘yan ta’addar Isra’ila suka kai, daga cikin wuraren tattalin arziki da shaguna 300, 45 ne kawai aka ba su izinin buxe ƙofofinsa, wasu kuma an rufe su da umarnin sojoji. Wannan na nufin babban asara ga tattalin arzikin Falasɗinu da ya riga ya yi rauni,” inji Shawesh.

Ya cigaba da cewa, “a wani mataki na tauye tattalin arzikin Falastinu, da kuma qara cin fuska, gwamnatin Isra’ila tana karvar haraji a madadinmu, ganin cewa suna da cikakken iko kan iyakokin ƙasar, sun hana kuɗaɗen haraji, wanda ya janyo gazawar gwamnatin Falastinawa wajen biyan albashi da ma masu ba da hidima.

Bayan kai hare-hare a kan asibitocin Gaza, kuma bayan shafe kwanaki da dama ana kai hare-haren, sojojin Isra’ila sun zo da wasu hujjoji jabu na ikirarin cewa ana amfani da cibiyoyin a matsayin sansanin soji.

“Abin baqin ciki, da hujjar jabu a kan asibitoci, da yawan ƙasashen yamma da shugabannin siyasa da kafofin watsa labarai har yanzu suna goyon baya da kuma cigaba da maimaita farfagandar ƙarya da zamba na Isra’ila.”

“A cikin jawabin da suka yi kan halin da ake ciki na jinqai a Gaza a gaban Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 17 ga watan Nuwamba, yawancin hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke aiki a yankunan Falastinawa da aka mamaye sun bayyana matuƙar damuwa game da abin da ke faruwa a Gaza.

“Mutane miliyan 1.6 sun rasa matsugunansu, daga cikin miliyan 2.2. Wannan dai shi ne gudun hijira mafi girma na Falastinawa tun shekara ta 1948, girman varna da asara yana girmama. An lalata dukkanin unguwannin ƙasar. Fiye da rabin rukunin gidaje a Gaza an ba da rahoton an lalata su”

“Aƙalla makarantun UNRWA 154 da sauran gine-gine ne aka mayar da su matsugunai. Yanzu mutane sama da 810,000 ne ke zama a ciki. Wato rabin mutanen da suka rasa matsugunansu,” inji Shawesh.