“Ina sa ran a siyasa na kai ga zama shugabar ƙasa”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Zainab Musa Ya’u, wata matashiya ce mai kimanin shekaru 22 da ta samu kai wa wani mataki na sarautar gargajiya da ba kasafai matasa masu ƙarancin shekaru irin nata suke samu ba. Rawar da take takawa a harkokin ƙungiyar raya al’adu da ɗaukaka kimar sarautun Ƙasar Hausa na Gamji Memorial Club a Jami’ar Jihar Gombe ya sa ta samun shiga a masarautar Gona da ke Ƙasar Akko, inda ta samu sarautar Giwar Matan Gona. A zantawar da ta yi da wakilin Blueprint Manhaja, Zainab ta bayyana masa cewa, ita sarauta dama gadon gidansu ce ba haye ta yi ba. Ta kuma bayyana burinta na watarana ta zama mace ta farko da za ta shugabanci Nijeriya bakiɗaya!
MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?
GIWAR MATAN GONA: Assalamu alaikum. Sunana Amb. Zainab Musa Ya’u. Haifafiyar Jihar Gombe daga yankin Gona a Ƙaramar Hukumar Akko. Ni ce Giwar Matan Gona, har wa yau kuma ni ce mai riƙe da sarautar Gimbiyar Gamji ta Jami’ar Jihar Gombe, inda nake ɗalibta a Tsangayar Nazarin Harshen Turanci. Ni jakadiya ce ta babbar Jami’ar Wisdom ta ƙasa da ƙasa, dalilin haka ne ya sa ake ambatona da laƙabin Ambasada. Ina cikin ƙungiyoyin ɗalibai daban daban, kasancewata mai kishin cigaban harkokin mata da matasa. Sannan kuma ni ƴar kasuwa ce da ke gudanar da sana’o’in dogaro da kai, da suka shafi mata. Ina kuma jagorantar shirin tallafa wa ƴammata da matan aure ƙananan sana’o’i da za su tallafa musu. Ina abubuwa da dama gaskiya.
Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taƙaice?
To, kamar yadda na faɗa a baya. Ni ƴar asalin Jihar Gombe ce, kuma an haife ni ne a nan cikin garin Gombe, a ranar goma ga watan Oktoba na shekarar 2001. Na yi karatun firamarena da sakandire duk a nan Gombe. Sannan yanzu haka ina aji na uku a Jami’ar Jihar Gombe, inda nake koyon harshen Turanci.
Na ji kin ambaci wasu sarautun gargajiya da ki ka ce kina da su, kamar Giwar Matan Gona da Gimbiyar Gamji, yaya aka yi ki ka samu waɗannan muƙamai duba da ƙarancin shekarunki?
To, da farko dai na samu sarautar Gimbiyar Gamji ne, sakamakon kasancewata a ƙungiyar raya al’adun gargajiya ta tunawa da Sardaunan Sakkwato, Sa Ahmadu Bello, wanda ake yi wa laƙabi da Gamji Ɗan Ƙwarai. Kusan a kowacce jami’a da ke arewacin ƙasar nan suna da irin wannan ƙungiyar ta ɗalibai, wanda duk shekara ake shirya bukukuwa na raya al’adun gargajiya daban daban, domin ƙara samar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ɗalibai.
Tun shigata makaranta na nuna sha’awata ta shiga wannan ƙungiya, saboda yadda nake son abubuwan sarauta, sakamakon kasancewata na fito daga gidan sarauta. Na riƙe muƙamai daban daban a ƙungiyar ciki har da Sarauniyar Matasa, sai kuma Gimbiyar Gamji da nake riƙe da ita har zango biyu a jere, saboda gudunmawar da nake bayarwa a harkokin ɗalibai a makarantar.
Mun ji yadda aka yi ki ka zama Gimbiyar Gamji to, ita kuma Giwar Matan Gona daga ina ki ka samo ta?
To, kamar yadda na faɗa a baya ina da alaƙa da gidan sarauta, kuma gwagwarmayata a harkar ƙungiyar Gamji ya sake ba ni ƙwarin gwiwa kan al’amarin sarauta. Mutane na yabawa da yadda nake shirya fita ta cikin kwalliya ta alkyabba da dawakai, makiɗa da maroƙa, yana burge mutane sosai. Saboda muna yin sa ne daidai da tsarin masarautun gargajiya na Ƙasar Hausa. Kuma lura da aka yi da irin gudunmawar da nake bayarwa ya sa ƴan Majalisar Sarki na fadar Mai Martaba Lamiɗon Gona suka ga dacewa sa cancantar a bani wannan sarauta ta Giwar Matan Gona, wacce kuma aka tabbatar min da ita cikin wannan shekara, 2023.
Yaya ki ka ji lokacin da aka ce an baki wannan sarauta ta Giwar Matan Gona?
Gaskiya ba qaramin farinciki na yi ba, domin kuwa ana gobe za a kawo min shaidar naɗin da za a yi min, kusan kwana na yi ban yi barci ba, saboda murna da zumuɗi. Kasan sarauta abu ne mai kwarjini da daraja. Sai ina ganin abin kamar a mafarki, yau ni ce za a bai wa sarauta daga masarautata. Na ji dadi marar misaltuwa.
Me za ki ce ga Lamiɗon Gona da ya karrama ki da wannan sarauta?
Gaskiya ban san irin kalmomin da zan yi amfani da su ba, wajen nuna godiya ga ubana, shugabana, kuma sarkina, Mai Martaba Sarkin Gona, Alhaji Umar Abdulƙadir Abdulsalam MNSI ba, saboda wannan gata da girmamawa da ya nuna min, ya zavo ni daga cikin ɗimbin mata, haziƙai da ake da su a masarautar Gona, ya bani wannan matsayi, don ya ƙara min ƙwarin gwiwa kan abubuwan da nake yi na raya al’adun gargajiya da sarauta. Na gode ƙwarai da gaske, godiya marar iyaka.
Yanzu da aka baki wannan sarauta, wacce gudunmawa ki ke ganin za ki iya bayarwa ga cigaban matan Gona?
Alhamdulillahi. Wannan babban abin yi wa Allah godiya ne. Kuma dama kamar yadda yake, a duk lokacin da ubangiji Allah Ya bai wa bawanSa wata babbar dama to, babu abin da ya kamata ga bawa irin ya yi ƙoƙari ya ga ya ba mara xa kunya, ya yi abin da ya dace, wanda jama’a za su yi alfahari da shi. In sha Allahu, na ƙudiri aniyar ganin na yi duk abin da zai kawo cigaba ga mata ba kawai a Gona ba, har ma da ɗaukacin Jihar Gombe da Nijeriya bakiɗaya, har ma da maza ba mata kaɗai ba. Kuma dama wannan gwagwarmaya ce da muka saba da ita, ba dare ba rana. In sha Allahu duk wani cigaba da na gani ko wata dama da na samu, zan yi ƙoƙari in ga na kawo wa jama’ar masarautata, cikin Akko da Gombe bakiɗaya.
A matsayinki ta matashiya, ba kya ganin wannan sarauta da aka baki ta Giwar Mata ta miki girma?
(dariya) E, gaskiya ne. Akwai wasu da suke ganin kamar wannan sarauta ba ta dace da ni ba, saboda na yi yarinya, wato suna ganin ina da ƙananan shekaru, wasu kuma na ganin ko aure ban yi ba, bani ya dace da wannan matsayi ba. Amma kuma ita sarauta da duk wani matsayi da mutum ya samu a rayuwarsa to, Allah ne Yake bayar da shi ga wanda Ya so. Ka ga ita sarautar Giwar Mata ai babbar sarauta ce da ake bai wa ƴaƴan cikin gida kaɗai, kuma a sarautun da ake bai wa mata kaf babu wacce ta kai darajar Giwar Mata. Ka ga kuwa dole a samu ƙalubale da ƙananan maganganu. Amma abin farinciki shi ne, shi Mai Martaba Lamiɗo Gona ya nunar musu da cewa, ai ita sarauta ba a yawan shekaru ko arziƙi take ba, cancanta ake dubawa a ga wane ne zai yi abin da ake buƙata, wanda zai iya kawo sauye-sauye da dabarun cigaba iri-iri. Wannan shi ya kwantar da maganganun da suka biyo baya a lokacin.
Kina ganin matasa suna da wata rawa da za su iya takawa ga cigaban harkokin sarauta?
Sosai ma kuwa, ai idan ka dubi akasari yanzu masarautun Ƙasar Hausa ana samun matasa sosai da ke riƙe da muƙamai daban-daban, wasu sarakunan masu kansu matasa ne. Saboda su ne masu sabbin jini da sabon tunani da ilimin zamani, waɗanda ake sa ran za su yi amfani da wannan damar tasu su kawo canji a masarautunsu. Babu shakka sanya matasa a harkokin sarauta yana qara dawo da martabar sarautun gargajiya, waɗanda ake ganin sun zama abubuwan tarihi kawai, sun zama tsohon ya yi, ba su da wani tasiri a zamanin yanzu. Kamar shi Lamiɗo Gona ai ka fa shi ma matashi ne, shi ya sa za ka ga yana ta shigo da sabbin abubuwa da za su ƙara dawo da martabar sarautar gidanmu, ta hanyar jawo wasu matasa da ya ga suna da gudunmawar da za su bayar.
Sannan kuma ka ga ita sarauta wata aba ce da ba ta son ƙasƙanci, kuma wannan ɗabi’a ce ta matasa. Kamar yadda ake son ado da kwalliya ta sarauta, wanda ke buƙatar kashe kuɗaɗe sosai, matasa ne kaɗai za ka ga suna da azamar yin haka, su cire maƙudan kuɗaɗe don ganin sun yi shiga ta musamman da za ta burge kowa. To, idan aka samu basaraken matashi za ka ga ya zo da sauye-sauye da dama da za su ƙara kwarjanta sarautar da yake yi, da shigo da sababbin abubuwa na cigaba.
Wanne goyon baya ki ke buƙata a wajen matan Gona da sauran jama’ar wannan masarauta?
Na san duk wanda ya fito daga Gona, yana alfahari da kasancewarsa ɗan wajen. Sannan kuma duk wani wanda ya samu wani matsayi na rayuwa, ba ya tava kai wa wani mataki sai tare da goyon bayan mutanensa. Na yi imanin ƴan’uwana da sauran jama’ar Gona za su cigaba da taimaka min da bani goyon baya ɗari bisa ɗari, don in kai ga cimma nasara a abubuwan da nake so in yi don cigaban wannan masarauta. In sha Allahu za mu sakanta alheri da alheri, ba za mu ba da kunya ba, bisa wannan yarda da ƙauna da aka nuna mana.
Ban da sarauta, wanne abu ne ki ke sha’awar ki ga kina yi a rayuwarki?
(Dariya) To, a gaskiya ban da sha’anin sarauta ina kuma sha’awar kasuwanci da harkokin siyasa sosai. Ina son wata rana nan gaba in shiga takarar siyasa don neman kujerar ‘yar majalisa ko a matakin jiha ko a tarayya. In sha Allahu, ni har kujerar shugaban ƙasa ina sa ran sai na kai gare ta.
Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?
Karin maganar da na fi saurin tunawa ita ce, ‘Yi Wa Wani Yi Wa Kai!’
Na gode.
Ni ce da godiya.
