Daga MUKHTAR YAKUBU
Ga duk masu karatun littattafan Hausa shekaru 40 da suka wuce ba za su manta da littafin ‘Turmin Danya’ na Sulaiman Ibrahim Katsina ba, wanda ya zo na ɗaya a gasar da ma’aikatar kula da al’adu ta tarayyar Najeriya ta shirya a 1982. Kuma yana daya daga cikin littattafan da aka saka a cikin manhajar karatun gaba da firamare, don haka duk wani ɗan makaranta a wancan lokacin ya san da wannan littafin da ma sauran masu karatun Hausa. Don haka ne ma ‘Turmin Ɗanya’ ya shahara a wajen masu karatun Hausa da manazarta.
Bayan tsawon shekaru, a yanzu Sulaiman Ibrahim Katsina wanda fitaccen ɗan Jarida ne a gidan rediyon BBC ya dawo da mallakar littafin ‘Turmin danya’ a matsayin mallakin sa, kuma an qara gyara shi tare da sake masa bango inda aka fitar da shi cikin tsari a ke sayar da shi a kasuwannin sayar da littattafai. Kan haka ne wakilin mu ya tattauna da shi domin jin tarihin rubutun littafin ‘Turmin Danya’ tun a wancan lokacin da kuma dalilin sa na sabunta littafin da karɓar haƙƙin mallakar sa, da yanzu haka har ya shiga kasuwa ana sayar da shi.
MANHAJA: Farko za mu so ka yi wa masu karatun mu ƙarin bayani a game da tarihin littafin ‘Turmin Danya’, samuwar sa da manufar yin sa, da kuma shekarar da aka fara buga shi.
SULAIMAN: To daman ina da niyyar rubutun littafin ‘Turmin Danya’, to sai kuma ga wata gasa, wadda ta ƙara mini ƙaimi. Ma’aikatar Kula da Al’adu ta Tarayyar Najeriya ce ta shirya ta, inda ta nemi a rubuta labari, ko wasan kwaikwayo ko kuma waƙe da Hausa. Ita kuma za ta wallafa wa waɗanda suka samu nasara. Allah da ikonsa sai ‘Turmin Danya’ ya yi na ɗaya. ‘Tsumagiyar kan Hanya’ na biyu, ‘Ƙarshen Alewa Ƙasa’ na uku. Kuma an wallafa ‘Turmin Danya’ da sauran su a 1982 .
Ko ya ya yanayin rubutun littafin da kuma saƙon da ya ƙunsa?
Na rubuta littafin ne a lokacin ina aiki. Don haka da yamma da kuma dare na fi yin rubutun. Kuma da hannu ne, wato da alƙalami, kana daga baya aka buga da keken rubutu (tafureta) sannan na aika shi Legas don shiga gasar lokacin gwamnati ba ta dawo Abuja ba.
Kuma labari ne na fasakwauri da cin hanci da rashawa da ba-takashi tsakanin masu fasakwaurin da jami’an tsaro da masu son kamanta gaskiya da waɗanda ba sa so, da tonon asiri a tsakanin su, da irin sharholiyar da ake ciki a wancan lokacin, akwai kuma wata soyayya ta ba-zata.
Ko yaya shaharar littafin da kuma irin moriyar da ka ci a littafin? Idan kuma ba ka ci moriyar sa ba me ya haifar da hakan?
Maganar shahara, sai in ce na ɗaya da ya yi, sai kuma makarantu da jami’o’i da ake amfani da shi. Cikin jami’o’in har da na ƙasashen waje. Wannan ce moriyar littafin da na samu. Amma a wajen kamfanin wallafa littattafai na NNPC, Zaria sun sha sake buga shi suna sayarwa a duk lokacin da ya ƙare.
Wani ya shaida mini cewa ko a watannin baya ya je kamfanin ya sayi littafina ɗaruruwa. ‘Turmin Ɗanya’ da ‘Tura ta Kai Bango’. Baya ga waɗanda su wakilan su NNPCn suke sayarwa a garuru.
Littafin mallakin NNPC ne, a yanzu an wallafa shi, kai a matsayin ka na marubucin littafin ‘Turmin Ɗanya’ ne ka buga shi, ko wani kamfani ne ya saya ko kuma kuka yi wata yarjejeniya da shi? Kuma idan haka ne ina maganar mallakar NNPC ta tsaya?
Shi ikon dukka mallakar littafi nawa ne, ikon wallafawa kuma na NNPC Zaria. Amma shi ‘Turmin Danya’ na karvi ikon wallafa shi daga hannun su na bai wa kamfanin wallafa na Gidan Dabino da ke Kano. Yanzu lauyoyina sun aika musu da wasiqar haramta musu wallafa wannan littafi da sayar da shi kai tsaye ko ta hannun dillalin su. Yanzu wannan wanda aka gyara, wallafar Kamfanin Gidan Dabino, shi ne kaɗai halastaccen da aka yarda a sayar da shi, duk wanda ya saya ko ya sayar da wancan na NNPC to ya karya doka.

A yanzu littafin ‘Turmin Danya’ an sabunta shi ne ta ɓangaren bango da shafuka, ko kuma da yanayin sa da aka sani a baya zai fito?
Kamar dai yadda na faɗa a baya ne. An ƙara gyara ƙa’idojin rubutun Hausar. Bugu da ƙari kuma an yi bayani a bangon cewa an qara gyara shi, an sauya hoto. Sannan manyan masana rubutu da kuma harshen Hausa sun tofa albarkacin bakin su a bayan bangon littafin.
Yanzu littafin ɗalibai na makatantu ne suka fi karanta shi, saboda an saka shi a tsarin karatu, ko akwai wani tsari da aka samar da kowa zai samu ya saya ya karanta?
Kwarai kuwa. A yanzu za a iya samun sa a kantunan sayar da littattafai a ko’ina a jihohin Arewacin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, sannan kuma za a rinƙa sayar da shi a kamfanin Gidan Dabino da ke Kano.
Akwai hanyoyin sayar da littattafai na zamani da ake da su a onlayin, ko shi ma ‘Turmin Danya’ za a saka shi a cikin wannan tsari?
Kwarai kuwa, akwai yiwuwar yin hakan nan ba da daɗewa ba in sha Allah.
To madalla mun gode.
Ni ma na gode sosai.
