Kotu ta bada umarnin sake zaɓe a mazaɓar Kakakin Majalisar Bauchi

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta bada umarnin kan a sake gudanar da zaɓen Ningi ta Tsakiya a Ƙaramar Hukumar Ningi, Jihar Bauchi.

Kakakin Majalisar Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, shi ne mai wakiltar Ningi ta Tsakiya a majalisar.

A zaman da ta yi a ranar Juma’a, Kotun ta bada umarnin a sake zaɓe a rumfunar zaɓe guda 10 a yankin.

Baturen zaɓe daga INEC, Farfesa Shuaibu Muhammad ne ya bayyana Suleiman a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Suleiman wanda ɗan Jam’iyyar PDP ne, ya lashe zaɓe a wancan lokacin ne da ƙuri’u 16, 866 inda ɗaɗa abokin hamayyarsa, Khalid Abdulmalik-Ningi na Jam’iyyar APC, wanda ya tsira da ƙuri’u 15, 065, sannan Danlami Bara’u na NNPP ya zo na uku da ƙuri’u 4,886 votes.

Rashin gamsuwa da sakamakon zaɓen ya sa Abdulmalik-Ningi garzayawa kotun sauraren ƙararrakin zaɓe neman a yi masa adalci. Amma kotu ta kori ƙarar tare da ayyana Suleiman a matsayin wanda ya yi nasara.

Haka shi ma ɗan takarar APC ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara don ƙalubalantar hukuncin kotun farko.

By Editor